Rundunar Sojin Hadin Gwiwa Ta 114 Sunyi Nasarar Dakile Wani Harin Kwanton Bauna Da Mayakan Boko Haram Suka Kai Masu Da Safiyar Yau

Rundunar Sojin Hadin Gwiwa Ta 114 Sunyi Nasarar Dakile Wani Harin Kwanton Bauna Da Mayakan Boko Haram Suka Kai Masu Da Safiyar Yau

- Harin kwantan bauna ba wani sabon abu bane ga Jami'an Sojojin

- Rundunar Sojojin hadin gwiwa na 26 dana 28 Sunyi nasarar dakile harin kwantan baunar

- Sojojin Sunyi nasaran kashe yan Boko Haram 18 da kuma raunata wasu daga cikinsu sannan sunyi nasarar kwace masu makamai

Sojojin hadin gwiwa na runduna ta 26 da 28 Sunyi nasarar wani dakile harin kwanton baunan da kungiyar Boko haram ta kai masu duk da yake harin kwanton bauna bawani sabon abu bane ga jami'an sojojin.

RUNDUNAR SOJOJIN HADIN GWIWA TA 114 SUN YI NASARAR DAKILE HARIN KWANTON BAUNA DA KUNGIYAR BOKO HARAM TA KAI MASU

RUNDUNAR SOJOJIN HADIN GWIWA TA 114 SUN YI NASARAR DAKILE HARIN KWANTON BAUNA DA KUNGIYAR BOKO HARAM TA KAI MASU

Kungiyar Boko haram ta kaiwa Sojojin harin kwanton baunar ne da Sanyin Safiyar yau a wasu wurare guda biyu da ake kira Pulka da Bitta dake cikin dajin Sambisa.

Sojojin Sunyi nasaran kashe mayakan Boko Haram 18 da kuma raunata wasu daga cikinsu, kuma sunyi nasaran kwace wasu makamai daga hannun yan'taaddan kamar yadda bayanin jami'in hukumar mai hulda da jama'a wato birgediya janaral, Sani Kukasheka Usman, ya ma yan jarida.

DUBA WANNAN: 'Yan Kungiyar IPOB Na Cikin Hadarin Rasa Rayuwar Su, Inji Kwamishinan 'Yan Sanda

Makaman da jami'an sojin suka yi nasarar kwacewa sun hada da bindigar AK-47 guda 11, bindigu masu sarrafa kansu guda 3, da wata samfurin bindiga ta musamman guda 1, da kuma motoci Hilux guda 2. Sauran sune Makamai masu linzami, da akwati 7 na alburusai.

Kukasheka, ya kara da cewa babu wani daga cikin Sojojin da ya rasa ransa illa kawai wasu da suka sami kananan raunuka, kuma yace sojojin a shirye suke da su karasa aikin su na kakkabe dajin sambisa da duk wani dan ta'adda da ke cikin dajin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel