An kafa Kotu na musamman domin barayi a Najeriya

An kafa Kotu na musamman domin barayi a Najeriya

- Yanzu mun ji an kafa Kotu na musamman domin barayin kasar nan

- Shugaban Alkalan kasar Onnoghen yace za ayi maganin masu sata

- Gwamnatin Buhari ta dage wajen yakar masu yi tattaki zagon kasa

Mun samu labari cewa an kafa wasu Kotu na musamman domin daure masu satar kudin Najeriya.

An kafa Kotu na musamman domin barayi a Najeriya

Alkalin Alkalai na kasa Walter Onnoghen

Shugaban Alkalan kasar nan Walter Onnoghen ya bayyana haka wajen kaddamar da manyan Lauyoyin kasar a Abuja. Jaridar Daily Sun ta rahoto cewa an kirkiro sababbin Kotu ne domin daure barayi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa.

KU KARANTA: Jonathan ya gargadi Lai Mohammed

Alkalin Alkalai na Kasar yace su na goyon bayan yaki da cin hanci da rashawa da waware kudin al'umma na Gwamnantin Buhari kuma su na bukatar hadin kan Jama'a. Onnoghen yace za a ware wasu Kotu na musamman domin shari'ar wadanda ake zargi sun yi gaba da kudin Kasa.

Wani mai taimakawa Shugaban kasa Buhari yace kowa ya san irin nasarar da Hukumar EFCC ta samu wajen karbe kudi daga hannun barayin kasar. Yace ko ba jima ko ba dade za a ga amfanin aikin da Gwamnatin Buhari tayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a b

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Lauyan Nnamdi Kanu yana jawabi a bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar suayin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel