Bayafra: Rundunar 'yan sanda tana tuhumar 'yan kungiyar IPOB guda 7 da kisan kai

Bayafra: Rundunar 'yan sanda tana tuhumar 'yan kungiyar IPOB guda 7 da kisan kai

- Ana zargin su da laifuka 12 ciki har da kisan Jami'in dan sanda da banka ma ofishin 'yan sanda wuta da kuma yin garkuwa da mutane

- Lauya mai kare wasu daga cikin wadanda ake zargi ya ce kotun majistare bata da ikon hukunci kan irin wadannan laifukan

- An hana lauyan belin da ya nema na wadanda yake karewa

Wata kotun majistare a Aba ta ingiza keyar wasu 'yan kungiyar IPOB zuwa kurkuku bisa zargin kisan kai da kona dukiyar jama'a. Wadanda ake zargi da wannan ta'adi sun hada da Chinonso Ude, Maduabuchi Echereodo, Ukochukwu Ikechukwu, Okechukwu Daniel, Okezie Jeremiah, Chizuruoke Nwanmuo da Ifeanyi Sunday.

Bayafra: Rundunar 'yan sanda tana tuhumar 'yan kungiyar IPOB guda 7 da kisan kai

Bayafra: Rundunar 'yan sanda tana tuhumar 'yan kungiyar IPOB guda 7 da kisan kai

An jefa su kurkukun ne sakamakon gabatar da su gaban kotun bisa zargin laifuka guda 12, ciki har da yin garkuwa da mutane da kashe jami'in dan sanda mai suna Cyril Nwosu da kuma banka ma ofishin 'yan sanda na Ariaria wuta har ma da motocin da ke haraban ofishin.

DUBA WANNAN: Shelkwatan tsaro DHQ sunyi dai-dai da suka kira IPOB yan ta'adda, Inji Sagay

Charles Onuchukwu, lauya mai kare wasu daga cikin wadanda ake zargi yayin neman belin su, yayi jayayyan cewa wannan kotun bata da ikon hukunci kan kisan kai da ta'addanci da satan mutane. Ya kuma ce bama ta da hurumin sauraron karan.

Alkalin kotun Ogbonna Adiele ya bayar da umurnin tasa keyar wadanda ake zargi zuwa gidan yarin Aba bayan ya gama sauraron korafin lauyan tsaf. Adiele ya kuma daga sauraron karan har zuwa 27 ga watan Satumba, 2017.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel