Biyafara: Cif wif na majalissar wakilai ya soki Saraki akan al’amarin Nnamdi Kanu, da IPOB

Biyafara: Cif wif na majalissar wakilai ya soki Saraki akan al’amarin Nnamdi Kanu, da IPOB

- Ado Doguwa yace maganar da Saraki yayi akan IPOB da Nnamdi Kanu faragandar siyasace kawai

- Saraki yace laka wa Nnmadi Kanu da kungiyar IPOB sunan yan ta'ada da rundunar sojojin Najeriya tayi ya saba kaidar dokar kasa

- Ana sa ran Buhari zai umarci rundunar sojoji su bar jihar Abia

Cif wif na majalissar wakilai, Alhassan Ado-Doguwa, ya kalubalanci shugaban majalissar dattawa, Bukola Saraki akan maganar da yayi na cewa laka wa yan kungiyan IPOB da Nnamdi Kanu sunan yan ta’ada ya saba ma dokar kasa.

Saraki yace: “Haramta kungiyan IPOB da gwamanoni kudu maso kudu suka yi da sanya su cikin jeriny kungiyoyin yan ta’ada da rundunar sojojin Najeriya ta yi, ya saba kundin tsarin Najeriya saboda ba su bi ka’ida ba.

“Duk lokacin da aka zantar da wani hukunci ba tare da bin ka’dia ba , wannan dokar ba za ta yi aiki ba. Na tabbatar da cewa shugaban kasa zai yi abun da yakamata.”

Biyafara : Cif wif na majalissar wakilai ya soki Saraki akan al’amarin Nnamdi Kanu, da IPOB

Biyafara : Cif wif na majalissar wakilai ya soki Saraki akan al’amarin Nnamdi Kanu, da IPOB

Ina kira da yan uwan mu dake kudu maso gabas, da su cigaba da zaman lafiya saboda rikici bai da amfani sai da ya saka rayukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba cikin hadari.

Ado- Doguwa ya mayar da martani da cewa maganar da Saraki yayi “ farfaganda ce na siyasace kawai.”

KU KARANTA : Biyafara: Jonathan ya ba Buhari laifi kuma soki Lai Mohammed

Na tabbatar da cewa maganar da shugaban majalissar datiijai yayi nuna son rai ne kawai, wanda bai da ce yayi halin yanzu ba.

“Sojoji Najeriya a nawa ra’ayin suna iya kokarin dan su ga an samar da zaman laifya da hadin kan yan Najeriya. Ko gwamnonin kudu maso gabas sun haramta abubuwan da Kanu da kungiyan IPOB su ke yi a yankin."

“A nawa ra’ayin maganganun da shugaban majalissar datiijai yayi siyasa ce kawai wanda ya nuna shi a matsayin shugaba mai wuyan sha’ani. Saboda inda akayi la’akari da harin da yan kungiyan IPOB sukai wa wanda basu ji ba ba su gani ba musamman yan Arewa, da kuma rawan da gwamnonin Arewa suka taka na tsayar da fargbar aukuwan wata rikici a Arewacin kasar, wannan ya nuna maganar da shugaban majalissar dattijai yayi ba dadai ba ne."

Duk da haka, a yau ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai umarci sojoji su bar jihar Abia.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel