IPOB: APC ta bukaci karin jihohi a yankin kudu maso gabashin kasar

IPOB: APC ta bukaci karin jihohi a yankin kudu maso gabashin kasar

- Jam'iyyar APC a jihar Enugu ta bukaci karin jihohi a yankin kudu maso gabas

- APC ta ce rashin kasancewar mutanen yankin a gwamnati ya jawo rikicin da ake ciki yanzu

- Mai magana da yawun jam'iyyar a jihar ya ce sun goyi bayan sake fasalin mulkin Najeriya don sake bunkasa tattalin arzikin ta

Jam'iyyar mai mulki ta APC a jihar Enugu ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi karin jihohi a yankin kudu maso gabas don maganta halin da ake ciki yanzu a yankin.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, jam'iyyar APC a yankin ta ce rashin kasancewar mutanen shiyar a gwamnati ya jawo wadannan matsalolin da ake ciki yanzu.

Mai magana da yawun jam'iyyar a jihar, Cif Osita Okechukwu, ya yi wannan kira a ranar Litinin, 18 ga watan Satumba a Enugu yayin da yake gabatar da matsayin yankin ga kwamitin APC akan sake fasalin kudin tsarin mulkin Najeriya.

IPOB: APC ta bukaci a yi karin jihohi a yankin kudu maso gabashin kasar

Wasu gwamnonin jam'iyyar APC

Okechukwu ya ce akwai bukatar kudu maso gabas ta samu karin jihohi don ta kasance tare da sauran yankuna kamar yadda aka tsara a taron kasa da aka yi a baya.

KU KARANTA: Gwamnonin Arewa 5 sun dira yankin Inyamurai da saƙon zaman lafiya

Ya ce, shiyar ta goyi bayan sake fasalin mulkin Najeriya don sake bunkasa tattalin arzikin kasar wanda shugaba Muhammadu Buhari ya ke jagoranta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shekaru 3 da Buhari yayi yana mulki yafi shekaru 16 da PDP tayi nesa ba kusa ba - Minista

Shekaru 3 da Buhari yayi yana mulki yafi shekaru 16 da PDP tayi nesa ba kusa ba - Minista

Shekaru 3 da Buhari yayi yana mulki yafi shekaru 16 da PDP tayi nesa ba kusa ba - Minista
NAIJ.com
Mailfire view pixel