Shelkwatan tsaro DHQ sunyi dai-dai da suka kira IPOB yan ta'adda, Inji Sagay

Shelkwatan tsaro DHQ sunyi dai-dai da suka kira IPOB yan ta'adda, Inji Sagay

- Ya ce dabi'un 'yan kungiyar IPOB din ya yi kama da na 'yan ta'adda

- Ya kuma ce jam'iyyar APC jam'iyya ce wacce ta kasa

- Sagay ya zargi wasu Alkalai da yiwa yaki da cin hanci da rashawa zagon kasa

A ranar Litini ne shuganan kwamitin masu ba shugaban kasa shawara kan yaki da cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagay, ya goyi bayan Hukumar Soji kan kiran 'yan kungiyar IPOB 'yan ta'adda duk da dai bai da tabbacin ko sun bi tsarin doka kafin su lakaba masu ta'addacin.

Sagay ya fada ma wakilin mu cewa dabi'un 'yan kungiyar IPOB din ya yi kama da na 'yan ta'adda idan aka yi la'akari da yanda suke tada hankula da zage-zage da kashe-kashe.

Shelkwatan rundunar soji sunyi dai-dai da suka kira IPOB yan ta'adda, Inji Sagay

Shelkwatan rundunar soji sunyi dai-dai da suka kira IPOB yan ta'adda, Inji Sagay

Ya ce inda ba don 'yan Arewa sun kame sun san ya kamata ba da IPOB ta saka kasan nan cikin halin tsaka mai wuya.

DUBA WANNAN: Buhari ya sha alwashin yakar cin hanci da har sai ta mutu

Sagay ya ce ba zai daina fadin ra'ayin sa ba don kare kasar nan duk da Sanatoci da 'Jam'iyyar APC sun matsa masa lamba. Ya kuma kira jam'iyyar a matsayin wacce ta kasa.

Sagay ya zargi wasu Alkalai da yiwa yaki da cin hanci da rashawa zagon kasa. A cewar sa samun nasara kan yaki da cin hanci da rashawan ba zai yiwu ba sai da hadin kan Alkalai.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel