Wa ya kashe Yar’Adua? Shehu Sani ya bukaci ayi sabon bincike a mutuwar tsohon shugaban kasar

Wa ya kashe Yar’Adua? Shehu Sani ya bukaci ayi sabon bincike a mutuwar tsohon shugaban kasar

- Sanata Shehu Sani ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya binciki ainahin musabbabin mutuwar marigayi shugaban kasa Umar Yar’Adua

- Yar’Adua ya rasu a ranar Litinin 5 ga watan Mayu, 2010 bayan dogon jinya

- Amma Sani ya bayyana cewa sabon labarin da ya zo kwanan nan ya nuna cewa mutuwar Yar’Adua ban a Allah bane

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari dabude sabon bincike a kan mutuwar marigayi shugaban kasa Umar Yar’Adua.

NAIJ.com ta tattaro cewa Sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Buhari ya tabbatar anyi binciken ainahin dalilin mutuwar Yar’Adua ba tare da bata lokaci ba.

Yace: “Da wannan sabon hujja da ya billo game da mutuwar Yar’Adua, shugaban kasa Buhari ya bude sabon binciki cikin ainahin abunda ya faru da marigayin shugaban kasar.

“Kafin yanzu a yarda cewa mutuwar tasa daga Allah ne, bayan dogon rashin lafiya, hujojin kwanan nan sun tabbatar da sabanin haka. Dole mu fayyace tarihin kwado. Me ya kashe shugaban kasa Umaru Yar’Adua sannan wa ya kashe Umaru Yar’Adua?"

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel