Biyafra: Gwamnonin Arewa sun yaba ma al'umma kan zaman lafiya

Biyafra: Gwamnonin Arewa sun yaba ma al'umma kan zaman lafiya

- Gwamnonin sun yi bakin ciki da hargitsin Jos amma sun yabawa Gwamnan Jihar Plateau

- Sun sanar da Jami'an tsaro da su zauna cikin shiri da jiran ko ta kwana

- Kundin tsarin mulki ya ba kowani dan kasa daman zama a ko ina cikin kasar nan in ji Gwamnonin

Gwamnonin Jihohi 19 na arewa sun yaba ma mutanen Arewa da kasancewa cikin zaman lafiya a yayin da hargitsi ke gudana tsakanin 'yan a ware na IPOB da Rundunar Soji, duk da kasancewa hargitsin ya sanya 'yan arewa mazauna Kudu cikin hatsari.

Gwamnonin sun yi kira ga mutanen dake fadin Jihohi 19 na Arewa kan su ci gaba da zaman lafiya suna me nuni da kuskuren gallazawa mutane. Gwamnonin sun yi wannan jawabi ne ta sakon email da Mallam Isa Gusau, mai ba Gwamnan Jihar Borno, Mista Kashim Shettima, shawara kan harkar sadarwa da dabaru, ya aika 'yan jarida. Shettima shine shugaban kungiyar gamayyar Jihohin Arewa.

Biyafra: Gwamnonin Arewa sun yaba ma al'umma kan zaman lafiya

Biyafra: Gwamnonin Arewa sun yaba ma al'umma kan zaman lafiya

Gwamnonin sun yi bakin ciki da hargitsin Jos amma sun yabawa Gwamnan Jihar Plateau kan yadda ya yi gaggawan magance matsalar. Sun sanar da Jami'an tsaro da su zauna cikin shiri da jiran ko ta kwana duk da yake dai mutane sun jajirce wurin tabbatar da zaman lafiya.

DUBA WANNAN: Bayafara: Ekweremadu, Gwamnonin kudu maso gabas da wasu hafsoshin soji sun shiga taro a Enugu (Hotuna)

Sun yi kira ga al'umma da su yi hakuri da juna su zauna lafiya koda akwai banbancin addini da kabila don samun cigaba. Suna kuma sanar da mutane cewan kundi tsarin mulkin kasan nan ya ba ko wani dan kasa daman zama a ko ina a fadin kasan. Sun kuma mika jajen su ga wanda hargitsin ya shafa.

A karshe Gwamnonin sun yi kira ga 'yan Arewa da ke zaune a sauran yankunan kasan nan da su kasance masu bin doka. Suna kuma kiran su da su kwantar da hankali suna masu tabbatar masu daukan mataki bisa doka don tallafa masu a ko wani hali suka tsinci kan su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel