Gwamna Ikpeazu ya gana da sarakunan gargajiya, sojin kasa akan Nnamdi Kanu

Gwamna Ikpeazu ya gana da sarakunan gargajiya, sojin kasa akan Nnamdi Kanu

Rahotanni daga shafin DAILY POST sun bayyana cewa, gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu, yayi ganawar sirrance tare da sarakunan gargajiya na jihar da kuma babban jami'i mai gudanar da harkokin sojin kasa a yankin Enugu, Manjo Janar A.B Abubakar.

A wani rahoto da sa hannun Enyinnaya Appolos, wanda shine babban sakataren ganawa da manema labarai na Gwmnan da kuma sa hannun sarakunan gargajiya, su na rokon babban jami'in sojin akan a rage yawan sojin dake jihar, musamman a garuruwan Aba da Umuahia don hakan yana hana al'ummomin yankin tsugunno.

Gwamna Ikpeazu ya gana da sarakunan gargajiya, sojin kasa akan Nnamdi Kanu

Gwamna Ikpeazu ya gana da sarakunan gargajiya, sojin kasa akan Nnamdi Kanu

Appolos ya kara da cewa, "Jami'an 'yan sanda da sauran jami'an tsaro su tabbatar da hana wadanda suke shigowa cikin jihar Abia daga wasu jihohin don magance tashin-tashina wanda zai janyo barazana ga zaman lafiya a cikin jihar."

KU KARANTA: Saudiya ta yankewa wani mahajjacin Najeriya watanni 3 a gidan Kaso

"Sarakunan gargajiya kuma su nemi hadin gwiwa tare da mai martaba Eze I. O Kanu ( Mahaifin Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar neman yankin Biyafara) don kawo hanyoyin dawo da zaman lafiya a yankunan."

"Sa'annan kuma yan jihar Abia da masu kasuwanci a jihar, su ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu kamar yadda suka saba, kuma su kauracewa shiga cikin masu tayar da zaune tsaye a jihar".

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel