Hukumar NDLEA ta kama wasu samari da safarar miyagun kwayoyi a Edo

Hukumar NDLEA ta kama wasu samari da safarar miyagun kwayoyi a Edo

- Hukumar NDLEA ta jihar Edo ta kama wasu samari 67 da safarar miyagun kwayoyi cikin jihar

- Samarin suna noman kwayar cannabis a garin wanda ke da babban hadari ga kayan abinci

- Kwamandan ya kira gwamnatin jihar da ta sa baki a lamarin

Hukumar National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) ta jihar Edo ta kama wasu samari 67 da safarar miyagun kwayoyi cikin jihar.

Kwamandar hukumar Mista Buba Wakawa, ya shaidawa gidan labaran NAN a ranar Alhamis a garin Benin.

Hukumar NDLEA ta kama wasu samari da safarar miyagun kwayoyi a Edo

Hukumar NDLEA ta kama wasu samari da safarar miyagun kwayoyi a Edo

A cikin mutanen da aka kama da zargin safarar kwayoyin ya hada da maza 47 da mata 29 ne a tsakanin watan Yuli zuwa Agusta.

Kimanin kwaya kilo 700 ne aka kama a dan tsakankanin lokacin. Kwayoyin da aka kama sun hada har da su cannabis sativa, hodar iblis da su heroine, tare da wata mota da suke safarar da ita.

Mista Wakawa ya bayyana yadda kwayoyin ke da hadari ga alumma kuma ya yi kira ga shugabanni da su sa baki a lamarin.

DUBA WANNAN: Daraktan wata ma'aikata ya kashe kan sa ta hanyar rataya

Kwamandan ya bayyana yadda samarin suka mamaye wani bangare a garin da noma kwayar cannabis wanda babban hadari ne ga kayan abinci, hakan ya sa ya yi kira ga gwamnatin jihar ta kawo dauki domin hadarin da yake tattare da noman kan ya zama ruwan dare a garin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel