Limaman Coci guda biyu sun sace yarinya yar shekara 2 a Kasuwa

Limaman Coci guda biyu sun sace yarinya yar shekara 2 a Kasuwa

Rundunar Yansandan jihar Legas ta gurfanar da wasu Fasto guda 2, Dorothy Ekutosi da Asekameh Victor, da suka sace wata karamar yarinya yar shekara 2 a Kasuwa.

A ranar Laraba 13 ga watan Satumba ne fastocin suka bayyana gaban kotun majistiri dake garin Ikeja, na jihar Legas, inda ake tuhumarsu da laifin hadin baki da kuma na sata, inji rahoton Daily Trust.

KU KARANTA: Rikicin Biyafara: Matasan IPOB na farautar Hausawa, sun ƙona motar Dangote (Bidiyo)

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito dansanda mai kara Inspekta Cliffor Ogu ya fada ma kotu cewa wanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 29 ga watan Agustan bana, a kasuwar Abule.

Limaman Coci guda biyu sun sace yarinya yar shekara 2 a Kasuwa

Wata kotu

“Mutanen nan su biyu sun yi hadin gwiwa tare da makbatar mahaifiyar yarinyar wajen sace karamar yarinyar, inda suka gudu da ita zuwa wani waje, suka boyeta.” Inji Dansandan.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito laifin yaci karo da sashi na 287 na kundin hukunta manyan laifuka, wanda ya tanadar da daurin shekaru 3 ga wanda aka kama da laifin.

Sai dai jin ta bakin dansanda mai kara, sai alkalin kotun ta bada belinsu akan naira dubu 100 kowanne, tare da masu tsaya musu. Sa’annan ta dage sauraron karar zuwa 20 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel