Biyafara: Abunda ya zama dole Buhari yayi ga kungiyar IPOB kan harin da suka kai ma Hausawa a Rivers - Ganduje

Biyafara: Abunda ya zama dole Buhari yayi ga kungiyar IPOB kan harin da suka kai ma Hausawa a Rivers - Ganduje

- Gwamnan jihar Kano ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi binciken hari da yan kungiyar Biyafara suka kai ma Hausawa a jihar Rivers

- Ganduje yace ya zama dole a hukunta masu laifi don guje ma sake afkuwar irin haka

- Ya kuma yaba wa matasan Arewa kan kokarinsu na son ganin hadin kan kasa

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi binciken hari da yan kungiyar Biyafara suka kai ma Hausawa a jihar Rivers.

Ganduje ya bayyana cewa idan ba’a hukunta wadanda suke da alhakin kai harin ba, irin haka zai kuma afkuwa.

Yayi kiran ne a lokacin da yake jawabi ga shugabannin kungiyar matasan Arewa wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a ofishin sa dake Kano.

Ganduje wanda ya bayyana cewa ba’a gyara barna da barna, yayi gargadi a kan yunkuri da ka iya haifar da sababbin hare-hare.

A cewar Ganduje: “Gwamnatin tarayya tayi gaggawan bincike kan hare-haren da yan Biyafara suka kai ma Hausawa a jihar Rivers sannan ta tabbatar da cewa an hukunta wadanda ke da alhakin kai harin.

"Idan ba’a hukunta wadanda ke da alhakin kai harin ba, al’amarin zai ci gaba da afkuwa sannan kuma zai iya haifar da wani mastala na daban.

“IPOB basu yi daidai ba hanyar magance matsala da rikici, sannan wannan baa bun watsar wa bane ta yadda wani zai haifar da rikicin da ka iya haifar da kisan kiyashin a kan wadanda basu san komai ba."

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Gwamna Ganduje ya gana da shugabannin Igbo a Kano a ranar Laraba

Gwamnan ya yaba ma matasan Arewa kan jajircewar su don ganin hadin kai a Najeriya.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Ganduje ya gana da shugabannin Igbo dake Kano don tabbatar masu da cewa zasu samu kariya daga gwamnatin jihar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel