Biyafara : Sojoji sun mayar da martani akan bidiyon da ya nuna ana cin zarafin yan kungiyan IPOB

Biyafara : Sojoji sun mayar da martani akan bidiyon da ya nuna ana cin zarafin yan kungiyan IPOB

- Manyan jami'an sojoji a sane suke da bidiyon

- An fara bicike akan bidiyon kuma za a bayyana ma al'umma sakamakon binciken

- Bidiyon ya nuna sojoji suna dukan yan kungiyan IPOB da bulala kuma sun sa wasu wanka da shan ruwan kwata

Rundunar sojojin Najeriya ta fara binciken wani bidiyon da ke yawo a shafikan sa da zumunta da ya nuna sojoji suna cin zarafin yan kungiyan IPOB.

Bidiyon mai tsawon minit 3, ya nuna tutar Biyafara a kasa da muntane a kwance fuskokin su na kallon kasa. Ya nuna sojoji suna dukan su da bulala kuma suka sa su wanka da shan ruwan kwata.

NAIJ.com ba za ta iya tabbtar da inganci tushen bidiyon ba, mai Magana da yawun sojoji Brigediya Janar Sani Usman, yace manyan jam’ian sojoji sun san da bidiyon.

Biyafara : Sojoji sun mayar da martani akan bidiyon da ya nuna ana cin zarafin yan kungiyan IPOB

Biyafara : Sojoji sun mayar da martani akan bidiyon da ya nuna ana cin zarafin yan kungiyan IPOB

"Ya fada ma manema labaru a daren Laraba cewa “A sane suke da bidiyon.”

KU KARANTA : Yanzu-yanzu : Likitoci sun dakatar da yajin aiki da ya dauki tsawon kwanaki 10

“Mun samu labarin bidiyon, kuma mun sa a fara binciken al’amarin, zamu bayyana ma al’umma sakamakon binciken.”

“Manjo janar Abubakar Adamu mai kula da rudunar 82 Division, ke jagoranatar binciken bidiyo kuma za’a bayyana ma al’umma sakamakon binciken.” Inji shi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel