Ana yi muna jin dadi - Wata kungiyar kabilar Ibo ta jinjinawa sojin kasa da suka dira a yankunan Kudu maso Gabas

Ana yi muna jin dadi - Wata kungiyar kabilar Ibo ta jinjinawa sojin kasa da suka dira a yankunan Kudu maso Gabas

Wata kungiyar ma'aikata ta yankin Kudu maso Gabas (The Southeast Professionals in Diaspora), ta jinjinawa sojin Najeriya, musamman ma sojin kasa akan kulla damarar yakar ta'addacin da ta ke yi a yankunansu, wadda a cewarsu 'yan kalilan ke tayar da zaune tsaye kuma wannan yunkuri na sojin zai maido da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali a yankin.

Shafin NAIJ.com ya ruwaito cewa, har ila yau, kungiyar tana baiwa sojin shawara akan tabbatar da kare lafiyar wadanda ba su ji ba ku ba su gani ba a cikin jihohin da dakarun ke gudanar da aikinsu, sannan kuma su tabbatar da kare hakkin al'ummarsu da dokokinsu.

Kakakin kungiyar Dakta Fidelis Nze KSM ya ce, sun yi murna ganin yadda gudanarwar soji mai taken rawar damatsiri ta biyu (Python dance II), ke samun nasarori wajen yakar ta'addaci a yankunan, duba da yadda masu tayar da zaune tsaye suke kawo tarzoma, musamman masu fafutukar neman yankin Biyafara wanda Nnamdi Kanu ke jagoranta, baya ga yadda suke adawa da kowace kabila a fadin kasar nan a yanzu.

Ana yi muna jin dadi - Wata kungiyar kabilar Ibo ta jinjinawa sojin kasa da suka dira a yankunan Kudu maso Gabas

Ana yi muna jin dadi - Wata kungiyar kabilar Ibo ta jinjinawa sojin kasa da suka dira a yankunan Kudu maso Gabas

Ya ke cewa, "wannan shi yake bayar da tabbacin samun canjin yanayi a yankunan, musamman kwananki kadan da suka gabata, lallai sojin Najeriya su na kokartawa, kuma tabbas da zarar an ci galaba akan ta'addaci a yankin kowa zai shiga taitayinsa, kuma al'amurra za su dawo bisa turbar tsari na kwanciyar hankali sannan kasuwanci ya cigaba da habaka".

KU KARANTA: Hukumar Fasa kauri ta yi nasarar datse wasu bindigu 1,100 a jihar Legas

Kungiyar ta na kira kuma ga gwamnonin yankin Kudu masoo Gabas, da su bayar da hadin kai da kuma goyon baya ga dakarun, da sauran jami'an tsaro don ganin an dawo da zaman lafiya a yankunan.

Kungiyar tana kara kira kuma ga jami'an tsaro akan su ci gaba da bincike mai zurfi wajen warware duk wani kulli da shirye-shiyen da kungiyar IPOB ke gudanarwa wanda Nnamdi Kanu ke gudanarwa.

Ta kara da cewa a kwanaki kadan da suka gabata, hukumar fasa kauri ta kasa ta datse wasu bindigu a sansanin ta na jihar Legas, kuma duba da yadda kungiyar ta IPOB suka kunno kai to tabbas akwai alamar tambaya dangane da shigowar wannan bindigu cikin kasar nan.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel