Rikicin Biafara: An kama 'yan banga 32, an kashe 'yan sanda 2

Rikicin Biafara: An kama 'yan banga 32, an kashe 'yan sanda 2

- Sun tari motar 'yan sanda har biyu, suka kwashe makaman ciki, kafin su banka musu wuta

- A harin 'yan sanda biyu sun rasa ran su, kuma sun raunata a kalla 3

- Su kuma an damki 32 daga cikin su, an ce sai sun fallasa wadanda suka arce

Kwamishinan 'yan sandan Ribas, Zaki Ahmed, ya ce an damke mutum 32 wanda ake zargin su da yin bangar Biafra a yankin karamar hukumar Oyigbo, wanda ya janyo har 'yan sanda biyu suka rasa ran su.

Rikicin Biafara: An kama 'yan banga 32, an kashe 'yan sanda 2

Rikicin Biafara: An kama 'yan banga 32, an kashe 'yan sanda 2

Ya gaya wa manema labarai cewa a hanzu haka sun wanzar da zaman lafiya a yankin, kuma ya sha alwashin duk wanda aka kama sai ya dandana kudar sa a hannun hukuma.

CP Ahmed ya karyata jita-jitar cewa wai an kona wani masallaci, amma ya gaskata cewa 'yan tarzomar sun bankawa wata motar 'yan sanda dake kan hanyar zuwa filin jirgin saman Fatakwal wuta.

"Sun raunata direban motar sosai, wanda a yanzu haka yana gadon asibiti. Sun kwashe makaman cikin motar kan su banka mata wuta. Da suka bar nan kuma, sun kara kona wasu motocin da shagunan mutane.

"Labari na zuwar mana sai muka yi gaggawar tura mutanen mu wajen, inda muka fasa taron kuma muka damki mutum 23.

"Muna barin wajen sai wadanda suka gudu suka sake haduwa suka afkawa wasu 'yan MOPOL da ke mahadar Oyigbo, inda a nan suka kashe dan sanda daya, Sajen Steven Daniel, kuma suka raunata biyu. Nan ma kwashe makaman cikin motar kafin su banka mata wuta.

DUBA WANNAN: Likitoci na so a hana yin tallan taba a Najeriya

"Nan take muka sake fita muka rufar musu har muka damke mutum 9, suka zama 32 kenan. Za muyi amfani da su don mu san sauran da suka arce don su ma mu kamo su. Da mun gama da su kuma zamu mika su ga kotu."

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel