CACOL ta lissafo ministoci 4 da ya zama dole Buhari ya dakatar da su

CACOL ta lissafo ministoci 4 da ya zama dole Buhari ya dakatar da su

- Kungiyar CACOL tayi kira ga gwamnatin Buhari da ta tsige wasu ministoci

- Kungiyar ta zargi ministocin da rashin kokari kamar yadda ya kamata

- Sun kuma bukaci shugabna kasa da ya bar kujerar a matsayin ministar man fetur

Kungiyar dake yaki da cin hanci da rahaswa ta CACOL tayi kira ga shugabna kasa Muhammadu Buhari da ya tsige wasu daga cikin ministocin sa.

A wata sanarwa daga shugaban kungiyar, Debo Adeniran, kungiyar ta lisaffo wasu ministoci wanda suke ganin basu tabuka wani abun kirkiba sannan sun yi kira ga a tsige su.

Musamman CACOL ta ambaci Babatunde Fashola, ministan wutar lantarki da gidaje, inda suka bayyana cewa ya gaza aikin sa.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Gwamna Ganduje ya gana da shugabannin Igbo a Kano a ranar Laraba

Sun kuma yi kira ga shugaba Buhari da ya sauka a matsayin ministan man fetur saboda ya maida hankali a al’amuran dake damun kasar.

Daga karshe sun nemi a sauke ministan shari’a, Abubakar Malami da kuma kudi Misis Kemi Adeosun a cewarsu dukkansu sun gaza a kan ayyukan su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel