Dalilin da yasa Gwamna Ganduje ya gana da shugabannin Igbo a Kano a ranar Laraba

Dalilin da yasa Gwamna Ganduje ya gana da shugabannin Igbo a Kano a ranar Laraba

- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilin ganawar gwamnan ta da shugabannin Igbo a jihar

- Jihar tace Abdullahi Ganduje ya gana da shugabannin don ba yan Igbo dake zaune a jihar tabbacin jajircewar sa wajen ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dore a jihar

- Ya kuma yi alkawarin cewa Igbo mazauna jihar Kano na cikin kariya

A ranar Laraba, 13 ga watan Satumba, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya gana da shugabannin Igbo a Kano.

A cewar daraktan labarai na Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, anyi ganawar ne domin tabbatar masu da kokarin gwamnatinsa na ganin an wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Yakassai ya wallafa a shafin twitter cewa: “Yanzun nan ai girma Gwamna Umar Ganduje ya gama ganawa da shugabannin Igbo a Kano don sake tabbatar masu da kokarinsa na wanzar da zaman lafiya/kwanciyar hankali a Kano.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Likitoci sun janye yajin aiki

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Gwamna Ganduje ya bayyana abunda zai faru da Igbo dake zaune a arewa.

Gwamnan yace dukkan Igbo mazauna jihar Kano zasu samu kariya daga ko wani rikici da ka iya taso wa.

Hakan ya biyo bayan wa’adin barin gari da wasu matasan arewa suka bay an kabilar Igbo dake zaune a yankin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel