Yanzu Yanzu: Likitoci sun janye yajin aiki

Yanzu Yanzu: Likitoci sun janye yajin aiki

- A safiyar ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba, kungiyar likitocin Najeriya NARD sun sanar da janye yajin aikin su

- An yanke shawarar ne bayan roko da dama daga gwamnati da al’umma

- Amma dai, likitocin sun ce zasu kara duba ga martanin gwamnati nan da makonni biyu

Kungiyar likitoci Najeriya a karkashin NARD sun a jiye yajin aikin da suke yi a safiyar yau Alhamis, 14 ga watan Satumba. Wannan hukunci na zuwa ne jim kadan bayan da shugabnnin kungiyar suka gana da juna.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, shugaban kungiyar reshen jahar Oyo, Segun Olaopa ya ce sun yanke hukuncin janye yajin aikin ne saboda rokon su da jama’a ke ta yi na cewar su baiwa gwamnati karin lokacin da za ta biya masu bukatunsu.

Ya ce bayan makonni biyu, za su tantance kokarin da gwamnati ta ke yi wajen cika alkawuran ta.

Yanzu Yanzu: Likitoci sun janye yajin aiki

Yanzu Yanzu: Likitoci sun janye yajin aiki

Tsakanin ranar Talata da Laraba ne dai kungiyar likitocin ta gana da gwamnatin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Najeriya ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta dakatar da rikicin kabilanci a Burma

Likitocin sun shiga yajin aiki ne a ranar 4 ga watan Satumba, al'amarin da ya haifar da cikas a asibitocin gwamnati a fadin kasar nan.

A nata bangaren, gwamnatin tarayya tace ta amince da bukatu da dama na likitocin, har da na biyan albashin da suke bin ta.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel