Yanzu-yanzu : Likitoci sun dakatar da yajin aiki da ya dauki tsawon kwanaki 10

Yanzu-yanzu : Likitoci sun dakatar da yajin aiki da ya dauki tsawon kwanaki 10

- A safiyar yau ne kungiyan likitocin Najeriya suka dakatar da yajin aiki

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta biya wasu daga cikin bukatun likitocin

- Kungiyan likitoci sun ba gwamnatin Najeriya makoni biyu dan su ga irin matakin da su dauka

Kungiyan likitocin Najeriya (NARD) sun sanar da dakatar da yajin aikin da suka yi na tsawon kwanaki goma

Sun dakatar da yajin aikin ne na tsawon makonni biyu dan su ga irin matakin da gwamnati zata dauka wajen cika akawarran da ta yi musu.

Shugaban kungiyan NARD reshen Ibadan, Segun Olaopa ya bayyana haka madadin kungiyan, a safiyar yau Alhamis bayan sunyi wani taron na gaggawa.

Yanzu-yanzu : Likitoci sun dakatar da yajin aiki da ya dauki tsawon kwanaki 10

Yanzu-yanzu : Likitoci sun dakatar da yajin aiki da ya dauki tsawon kwanaki 10

Yace “An yanke shawarar ne bayan kira da al’umma suka yi wa likitoci da su ba gwamnatin tarayya karin lokaci don biya musu bukatunsu."

KU KARANTA : NLC ta yi alkawarin tona asirin gwamnonni da sukayi almundahana da kudin Paris Club

“Za mu ba gwamnati mako biyu dan muga irin matakin da za su dauka wajen cika alkawaran da suka yi mana."

Yajin aiki da likitoci suka fara tun 4 ga watan Satumba, ya durkusar da ayyuka a asibitoci gwamnati dake fadin kasar.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta biya wasu daga cikin bukatan likitocin, ciki hadda matsalar albashi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel