Labari da duminsa: Gwamna Ikpeazu ya kara tsawaita dokan hana fita a jihar Abia

Labari da duminsa: Gwamna Ikpeazu ya kara tsawaita dokan hana fita a jihar Abia

- Dokar ta kullen ta tashi daga kwana 3 zuwa kwana 4 saboda yanayi na tsaro

- Ikpeazu ya yi kira ga mazauna jihar da kuma baki da su ba jami'an tsaro hadin kai don tabbatar da doka da oda

- Ya kuma yi kira ga jami'an tsaron da su daina musgunawa mutane yayin wucewan su ta wurarren bincike

Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya ja dokar hana fita da ya kafa na kwana 3 a Aba, cibiyar kasuwancin jihar, zuwa ranar Juma'a 15 ga watan Satumba. Ya shawarci mazauna jihan da kuma baki da su ba jami'an tsaro hadin kai don tabbatar da doka da oda a garin.

Gwamna Ikpeazu ya kara tsawaita dokan hana fita a jihar Abia

Gwamna Ikpeazu ya kara tsawaita dokan hana fita a jihar Abia

A wani jawabi da Gwamnan ya yi ta bakin sakataren sa na yada labarai, Enyinnaya Appolos, ya nuna damuwar sa kan yadda jami'an tsaro suke sa mutane daga hannayen su yayin wucewa ta wurarren bincike.

DUBA WANNAN: Gwamna Ikpeazu ya sanya dokar hana fita a Aba yayin da sojoji suka dira a garin

Ya yi kira ga jami'an tsaron da duk wanda wannan al'amari ya shafa da su yi gaggawan daina wannan tozarci da duk wani nau'in musgunawa.

Tun da fari dai Gwamnan ya saka dokar ta hana fita saboda hali na tsaro da toshe wata kafan ballewar hatsaniya. Da fari dai Dokar na kwana 3 ne daga maraice zuwa safe, daga ranar Talata 12 ga watan Satumba zuwa ranar Alhamis 14 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel