Mun kamalla shirye-shiryen taso keyar Diezani zuwa Najeriya - Hukumar EFCC

Mun kamalla shirye-shiryen taso keyar Diezani zuwa Najeriya - Hukumar EFCC

- An gama shirye shiryen taso keyarta daga turai zuwa gida Najeriya kan tuhumar laifukan cin hanci d a rashawa

- An zo matakin da babu wanda ya isa ya hana yaki da cin hanci da rashawa

- An kira da jama'a su tona duk wani jami'in EFCC da ke cin hanci da rashawa

A ranar laraba ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, ta tabbatar da shirye shiryen taso keyar tsohuwar Ministan man ferur, Diezani Alison Madueke zuwa Najeriya don fuskantar hukunci. 'Yan Najeriya da dama sun bukaci a taso keyar ta daga turai ganin yadda aka tuhuman ta da laifukka da dama na cin hanci da rashawa.

Mun kamalla shirye-shiryen taso keyar Diezani zuwa Najeriya - Hukumar EFCC

Mun kamalla shirye-shiryen taso keyar Diezani zuwa Najeriya - Hukumar EFCC

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Laraba. Tuni dai gwamnati ta kwace wasu daga cikin kaddarorin ta. ''Ina son ku sani cewa babu wanda zai tsallake hukunci. Muna ma shirin taso keyar Diezani ne alhali bincike yana gudana''. In ji shi.

DUBA WANNAN: Yadda shugaba Buhari ya kamata ya gudanar da sharia'ar Diezani - Stella Oduah

Ya kara da cewa ''mun kawo matakin da babu wanda ya isa ya hana mu yakin cin hanci da rashawa amma dole mu fahimci cewa wannan yaki ya shafe mu ne gaba dayan mu don cigaban al'umma mai tasowa''.

Magu ya ce cin hanci da rashawa ne silan gwagwarmayar neman raba kasa da yajin aiki da sauran tsiyatakun da suka wa kasar kanta. Ya ce hakkin mu ne mu gyara duk wani abu da cin hanci da rashawa ya lalata.

Magu ya ce tarbiyya daga gida take fatawa. Don haka ya yi kira da a fito fili a sanar da su game da duk wani jami'in hukumar ta su ta EFCC da ya jefa kan shi cikin lamarin cin hanci da sharawa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel