Rikicin Biyafara: Matasan IPOB na farautar Hausawa, sun ƙona motar Dangote (Bidiyo)

Rikicin Biyafara: Matasan IPOB na farautar Hausawa, sun ƙona motar Dangote (Bidiyo)

- Yayan kungiyar neman kafa kasar Biyafara, IPOB sun bazama farautar Hausawa

- Matasan Inyamurai sun fara far ma Hausawa a garin Abia da Fatakwal

Biyo bayan barkewar rikici tsakanin Sojojin Najeriya da yayan kungiyar rajin samar da kasar Biyafara, IPOB, garin Aba dake jihar Abia, yan kungiyar sun afka ma Hausawa.

Wani bidiyo da yayi yawo a shafukan sadarwa na zamani ya nuna yadda matasan Iyamurai ke tsayar da motoci suna farautar Hausa-Fulani Musulmai, yayin da suka kona motoci da shagunan su.

KU KARANTA: El-Rufa’i ua tare da Sarkin Zazzau a taron gwamnoni da Sarakuna a Kaduna (Hotuna)

NAIJ.com ta ruwaito mutanen cikin motar suna yin magana da yaren Ibo, suna cewa su fa Inyamurai ne, kuma babu Hausawa a cikinsu, don haka su kyale su, su yi tafiyarsu.

Rikicin Biyafara: Matasan IPOB na farautar Hausawa, sun ƙona motar Dangote (Bidiyo)

Matasan IPOB yayin da suke farautar Hausawa

Duk a cikin bidiyon an hangi matasan suna dauke da makamai, da suka hada da adduna, katakwaye da sauransu, haka zalika an hange abubuwa da dama akan hanya da suka kokkona, ciki har da motar Dangote.

Ga bidiyon a nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel