Rikicin Biyafara: Sojojin Najeriya sun tumurmusa ýan IPOB, sun kashe 1 (Hotuna/Bidiyo)

Rikicin Biyafara: Sojojin Najeriya sun tumurmusa ýan IPOB, sun kashe 1 (Hotuna/Bidiyo)

Wani faifan bidiyo ya watsu a kafafen sadarwa, wanda shafin Sahara Reporters ta ruwaito, wanda ke nuna wasu Sojoji suna azabtar da wasu matasa yayan kungiyar IPOB.

A yan kwanakin nan dai an samu barkewar rikici a wasu jihohin yankin Inyamurai, musamman a garin Abia, inda shugaban kungiyar rajin samar da kasar Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu ke zaune, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

KU KARANTA: Diyar shugaban kasa, Hanan Buhari tayi bajakolin basirarta a wani ƙasiataccen taro (Hotuna)

Da fari dai Sojoji ne suka yi faretin nuna kwanji a garin Umuahia, don tsoratar da yana kungiyar IPOB dake kokarin tayar da hankula a wannan yanki, inda daga nan aka samu takaddama tsakanin IPOB da Sojoji, wanda aka ruwaito hakan yayi sanadiyyar jikkata wasu yan kungiyar.

Rikicin Biyafara: Sojojin Najeriya sun tumurmusa ýan IPOB, sun kashe 1 (Hotuna/Bidiyo)

Sojojin Najeriya da ýan IPOB

Sai dai hakan bai yi ma yan IPOB din dadi ba, inda suka bazama suna kona shagunan Hausawa tare da hallaka wasu daga cikinsu, sanadiyyar wannan, gwamnan jihar Abia, bai yi wata wata ba, ya kaddamar da dokar ta-baci a garin Umuahia, ba shiga,ba fita.

Rikicin Biyafara: Sojojin Najeriya sun tumurmusa ýan IPOB, sun kashe 1 (Hotuna/Bidiyo)

Sojojin Najeriya sun tumurmusa ýan IPOB

A cikin wannan bidiyon zaku ga yadda Sojoji suka kama wasu yan IPOB da suka karya dokar ta bacin, inda suka basu horo mai tsanani, kuma za’a hangi gawar daya daga cikinsu, tare da muryar wani yana tabbatar da mutuwar mutumin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel