Abuja: Majalisar Tarayya ta jinkirta dawowar ta da mako daya

Abuja: Majalisar Tarayya ta jinkirta dawowar ta da mako daya

- Majalisar Tarayya ta kasa ta jinkirta dawowar ta da mako daya daga ranar Talata 19 zuwa Talata 26 na watan Satumba

- Ya kamata ‘yan majalisar su dawo bakin aiki ne a ranar Talata, 19 ga watan Satumba

- Sanarwara ta bukaci dukkanin 'yan majalisar tarayya su dawo a ranar Talata, 26 ga Satumba a daidai karfe 10 na safe

Majalisar tarayyar Najeriya ta jinkirta dawowar ta daga hutu da mako daya.

‘Yan majalisar wadanda ya kamata su dawo bakin aiki a ranar 19 ga watan Satumba, amma yanzu haka sun jinkirta dawowar har zuwa ranar 26 ga Satumba, 2017.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, wannan ya ƙunshi cikin sanarwa wanda Clerk na majalisar tarayya, Mista Mohammed Sani-Omolori ya yi a ranar Laraba, 13 ga watan Satumba.

Abuja: Majalisar Tarayya ta jinkirta dawowar ta da mako daya

Majalisar Tarayyar Najeriya

Sanarwa ta ce, "Wannan shi ne sanar da dukkanin 'yan majalisar dattijai da na wakilai cewa an jinkirta dawowar su aiki daga ranar Talata 19 ga Satumba zuwa Talata 26 Satumba 2017”.

KU KARANTA: Dino Melaye a cikin Khakhi ya ce 'ya shirya wa ko wane mugun mutum' (Hotuna)

"An bukaci dukkanin 'yan majalisar tarayya su dawo a ranar Talata, 26 ga Satumba a daidai karfe 10 na safe”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel