NNPC za ta rufe wasu matatan mai 3 a Najeriya don gudanar da gyare-gyare

NNPC za ta rufe wasu matatan mai 3 a Najeriya don gudanar da gyare-gyare

- Kamfanin albarkatun man fetur ta kasa ta ce zata rufe matatan mai uku don gudanar da gyare-gyare a kansu

- Babba darektan NNPC Ya ce gyare-gyaren matatan mai zai mayar da su kamar sabuwa

- Ana sa ran za a kammala gyaran a shekara ta 2019

Kamfanin albarkatun man fetur ta kasa (NNPC) ta sanar da cewa za ta rufe wasu matatan mai uku don gudanar da gyare-gyare.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, babban daraktan NNPC, Dokta Maikanti Baru, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Satumba a wani taro wanda kungiyar bututun mai ta Najeriya (PLAN) ta shirya.

Yace gyare-gyaren da za a yi zai sake mayar da matatan mai Warri da Kaduna da kuma Fatakwal kamar sabuwa.

NNPC za ta rufe wasu matatan mai 3 a Najeriya don gudanar da gyare-gyare

Kamfanin albarkatun man fetur ta kasa (NNPC)

Baru ya ce: “Kamar yadda kuka sani cewa mutane na tunanin cewa ba a taɓa yin cikakken gyara ba; don haka a wannan lokaci nufin mu shine mu rufe matatan mai da gyaran ta shafa don gudanar da ingantacen aiki”.

KU KARANTA: NLC ta yi alkawarin tona asirin gwamnonni da sukayi almundahana da kudin Paris Club

"Muna nufin za mu mayar da hankalinmu a kan gyaran matatan mai tare da duk abin da suke bukata don tabbatar da cewa a lokacin da aka kammala a shekara ta 2019, wadannan matatan mai za su kasance masu kyau kamar sabo" in ji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel