Allah Sarki: An tura keyar wani matashi zuwa gidan kaso a kan satar amalanke

Allah Sarki: An tura keyar wani matashi zuwa gidan kaso a kan satar amalanke

- Wani matashi ya bakonci gidan kaso a kan zargin sata amalanke

- Wannan lamarin ya faru ne a Mechanic Village dake Isolo

- Hukumar ‘yan sanda na Aswawani suka gabatar da matashin a gaban kotun Majistare da ke Isolo

Wannan lamari mai ban mamaki ga wani matashi marasa aikin yi mai shekaru 26, Mista John Chima wanda yake ƙoƙari ta hanyar neman abin da zai ci. An tattara cewa aikin da Chima ya so ya shiga yana buƙatar amalanke, don haka sai ya saci daya bayan da ya kasa samun wanda zai taimaka masa saya.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, wannan al’amarin ya yi sanadiyar da akakai Chima kurkuku bayan da aka kama shi tare da tsohon amalanken kuma aka mika shi ga jami’an 'yan sanda wanda suka gurfanar da shi a kotu. Wannan lamarin ya faru ne a Mechanic Village dake Isolo, inda ake zargin an sace abin.

Jaridar P.M.EXPRESS ta ruwaito cewa duk ƙoƙari na warware matsalar a ofishin ‘yan sanda da ke Aswani ba ta cimma wani nasara ba yayin da 'yan sanda suka nace cewa ya aikata laifi kuma ya kamata a hukunta shi.

Allah Sarki: An tura keyar wani matashi zuwa gidan kaso a kan satar amalanke

Wani matashi da aka zargi da sata amalanke

Wanda ake tuhuma ya bayyana wa 'yan sanda cewa ba wai ya sace amalanke ba ne, amma yana buƙatar amalanken ne don aikinsa kuma ba shi da kuɗin saya don haka ya sa ya dauki wannan.

KU KARANTA: Boko Haram: Ko Kun San Me Gwamnati Ke Yi Da Tubabbun Mayakan Kungiyar Boko Haram?

Bayan haka aka gabatar da Chima a gaban kotun Majistare a Isolo, kuma aka yi masa tuhuma sata wanda ta sabawa doka. Amma ya ki aminceda laifin.

Mai gabatar da kara, Mista Oje Uagbale ya nemi kotun ta ba Chima beli ta yadda zai ci gaba da zuwa kotun don fuskantar shari’a.

Babban alkalin kotun, Mista O.A Ogbe ya ba shi beli na naira 50,000. Amma aka kai shi kurkuku saboda babu wanda ya za belinsa a kotun. An dakatar da batun har zuwa 18 ga Satumba, 2017.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince

Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince

Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince
NAIJ.com
Mailfire view pixel