Gwamnonin APC sun kai ziyarar jaje ga al’ummar jihar Benuwe

Gwamnonin APC sun kai ziyarar jaje ga al’ummar jihar Benuwe

Gwamnonin jam’iyyar APC, karkashin inuwar kungiyar gwamnonin jam’iyar sun kai ziyarar jaje ga al’ummar jihar Benuwe, sakamakon ibtila’in daya afka musu a kwanakin baya.

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom ne ya tarbi tawagar gwamnonin da suka kawo masa ziyarar, a karkashin jagorancin shugaban kungiyar, gwamna Rochas Okorocha tare da takwaransa na jihar Kebbi, Atiku Bagudu.

KU KARANTA: Diyar shugaban kasa, Hanan Buhari tayi bajakolin basirarta a wani ƙasiataccen taro (Hotuna)

Ana sa ran gwamnonin zasu yi ma matsalar ambaliyar ruwan karatun ta natsu, don gano hanyoyin da zasu bada gudunmuwar kare sake afkuwar hakan.

Gwamnonin APC sun kai ziyarar jaje ga al’ummar jihar Benuwe

Gwamnonin APC

A wani labarin kuma, an nada hamshakin attajiri, Aliko Dangote shugaban kwamitin bada agajin gaggawa ga wadanda lamarin ya shafa, Dangote ya bada kyautan naira miliyan 250 ga kwamitin, baya da taimakon daya baiwa gwamnatin jihar Anambra na N150m.

Rahotanni sun tabbatar da sama da mutane 110,000 ne suka samu kansu cikin mawuyacin hali, tare da mutuwar mutane 3 a sanadiyyar ambaliyar data mamaye garuruwansu, cikin har da babban birnin jihar, Makurdi.

NAIJ.com ta ruwaito wajajen da ambaliyar yafi shafa suna hada da Achusa, Idye, Welfare Quarters, Mobile Barracks, New Kanshio Layout, Wadata market, Wurukum market, Gyado villa, Kucha Utebe, Breweries, Nyiman layout, Behind Civil Service Commission, Radio Benue, Industrial layout, BIPC quarters, Uniagric road, Katungu, Genabe, Behind Officon, UAgboughul- wadata da Demekpe communities.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel