Lokoja: ‘Yan majalisar dokokin jihar Kogi sun bukaci kotu ta aika shugabansu gidan yari

Lokoja: ‘Yan majalisar dokokin jihar Kogi sun bukaci kotu ta aika shugabansu gidan yari

- Wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Kogi sun kai karar gwamnan jihar da shugaban majalisar a babbar kotun jihar

- ‘Yan majalisar sun bukaci kotu ta aika shugaban majalisar dokokin jihar zuwa gidan yari

- Babbar kotun jihar ta umurni biyan Hon. Friday Sani Makama kudin alawus da albashi na tun lokacin da aka dakatar da shi

Tsohon shugaban 'yan tsiraru na majalisar dokokin jihar Kogi da memba mai wakiltar mazabar Igalamela / Odolu Hon. Friday Sani Makama sun halarci babbar kotu na jihar yayin da suka bukaci kotun ta aika shugaban majalisar, Hon. Matiyu Kolawole zuwa gidan yari.

A cikin wadanda aka kai karar sun hada da gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello da kwamishinan shari'a da kuma Hon. Godwin Osuyi.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, Makama ya yi ikirari ta hanyar lauyarsa, J. S. Okutepa (SAN) cewa masu amsa sun saba wa shari’a da kotun ta yanke na sake dawowa da shi da kuma biyan shi kuɗaden alawus da albashi.

Lokoja: ‘Yan majalisar dokokin jihar Kogi sun bukaci kotu ta aika shugabansu gidan yari

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello

Idan baku manta ba babbar kotun jihar Kogi da ke zaune a Lokoja ta gabatar da hukuncin sake mayar da Makama a ranar 29 ga watan Yuni, 2017.

KU KARANTA: Yadda shugaba Buhari ya kamata ya gudanar da sharia'ar Diezani - Stella Oduah

Kotun ta kuma umurni biyan shi duk kuɗin alawus da albashi tun lokacin da aka dakatar da shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel