Gwamnatin Najeriya ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta dakatar da rikicin kabilanci a Burma

Gwamnatin Najeriya ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta dakatar da rikicin kabilanci a Burma

Gwamnatin tarayya tayi Allah wadai da mumunar hali da yan kabilan Rohingya suke fuskanta a Burma.

Wasu yan kabilan Rohingyas 370,000 sun tsere daga yankin yamman Rakhine zuwa Bangladesh a yan makonni, a cewar majalisar dinkin duniya.

Rikicin ya barke ne a 25 ga watan Agusta, bayan mayakan Rohingya suka kai hari kan yan sanda, wanda yayi sanadiyar aikawa da rundunar soji.

Gwamnatin Najeriya ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta dakatar da rikicin kabilanci a Burma

Gwamnatin Najeriya ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta dakatar da rikicin kabilanci a Burma

Shugaban hukumar kare hakin bil’adama Zeid Raad Al-hussein yace a ranar Litinin jami'an tsaro a Rakhine suka bayyana a matsayin “misalin littafi dake tsarkake kabilu”.

Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, a wani jawabi da ya gabatar jiya, yace kasar Najeriya tana jajenta al’amarin cin zarafi da ake a kan mutanen Rakhine.

KU KARANTA KUMA: Kada ku tunzura ta hanyar kai hare-haren fansa – Matasan Arewa sun yi gargadi

Yace rikicin “tunatarwa ne ga abunda ya faru a Ruwanda a 1994 da Bosnia Herzegovina a 1955.”

Gwamnatin tarayya tayi Allah wadai da mumunar halin cin zarafin mutane wanda wani babban kwamishinan majalisar dinkin duniya yayi jawabi a kai yau, ministan yace al’amarin ya kasance “misalin littafi dake tsarkake kabilu” na mutanen Ruhingya”.

Yayi kira ga majalisan dinkin duniya ta kaddamar da ka’idan ”Alhakin kare rayuka” da sa baki a al’amarin Burma don tsayar da yakin tsarkake kabilu da kirkiran sharruda da zai tabbatar da dawowar wadanda suka tsere daga Rohingya cikin koshin lafiya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel