Cibiyar kawo dauki na gaggawa tana ankarar da gwamnati da masu ruwa tsaki akan ambaliyar ruwa

Cibiyar kawo dauki na gaggawa tana ankarar da gwamnati da masu ruwa tsaki akan ambaliyar ruwa

Mista Yunusa Maihaja, wanda shine shugaba na cibiyar kawo dauki cikin gaggawa (National Emergency Management Agency, NEMA) ya ankarar da gwamnatin jihohi da kuma masu ruwa da tsaki akan zama cikin shiri domin akwai yiwuwar faruwar ambaliyar ruwa dag Jamhuriyyar Nijar.

Maihaji ya yi wannan sanarwa ne a ranar Laraba ta yau a wurin taron wayar da kai tare kungiyar majalisar dinkin duniya wato United Nations akan ambaliyar da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

A cewar Maihaja, anyi wannan taro ne domin shiryawa da kuma fadakar da yankunan da ake bukatar su zama cikin shirin wannan ibtila'i.

A jawabinsa, "tafkuna da kuma ma'adanan ruwa domin amfani noman rani da samar da wutar latarki musamman ma na yankunan Benue, Lokoja, da Kebbi sun cika sun batse kuma akwai ragowar Dam din Kainji, Jebba da Shiroro wanda su har sun fara malalo ruwa sanadiyar tsananin cika da suka yi."

Cibiyar kawo dauki na gaggawa tana ankarar da gwamnati da masu ruwa tsaki akan ambaliyar ruwa

Cibiyar kawo dauki na gaggawa tana ankarar da gwamnati da masu ruwa tsaki akan ambaliyar ruwa

"A bisa kiyasin mu yanzu, akwai jihohi 27 wanda suka yi kacibus da ambaliyar ruwa da kuma jihohi 10 wanda ruwan mai karfi ya jefa cikin wani hali a fadin Najeriya."

KU KARANTA: Jihar Kano ta dauki aniyyar yakar fataucin miyagun kwayoyi

Maihaja ya ce, "tun a bayan cibiyar NEMA ta yi gargadin jihphi 26 da aka kiyasta yiwuwar samun ambaliyar cikin wannan shekara, wanda cibiayar ta rinka yadawa a gidajen talabijin da rediyo."

Shugaban NEMA ya na kira ga gwamnatin jihohi da kuma masu ruwa da tsaki akan su zama cikin shirin wannan kiyasi da aka gunadanar akan yiwuwar faruwar ambaliyar ruwa, wanda hakan zai tseratar da dukiyoyi har ma gujewa rasa rayuka.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel