Hausawa a Ribas sun nemi mafaka a ofishin ‘yan sanda bayan wani rikici da IPOB

Hausawa a Ribas sun nemi mafaka a ofishin ‘yan sanda bayan wani rikici da IPOB

- An samu baraka tsakanin Hausawa mazaunar jihar Ribas da ‘yan kungiyar IPOB

- Bayan barkewar rikicin Hausawa sun nemi mafaka a ofishin ‘yan sandan jihar

- Wani mai suna Victor Ezeanochie ya wallafa hoton Hausawa yayin da suke zaune a ofishin ‘yan sanda a yanar gizo

Wasu Hausawa 'yan asalin yankin arewa sun nemi mafaka a ofishin ‘yan sanda na Umuebulu da ke jihar Ribas, in ji Victor Ezeanochie wanda ya wallafa hoton mutanen a yanar gizo.

Wannan al’amarin ta faru ne bayan da wasu 'yan kungiyar IPOB da ake zargi sunkai hari a kan al’ummar Hausawa mazaunar jihar a ranar Talata, 12 a yankin karamar hukumar Oyibo na jihar Ribas.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, aukuwar lamarin ya fara ne lokacin da 'yan kungiyar IPOB da ake zargi sun taru a Timber Junction yayin jiran sauran membobin ‘yan kungiyar don zuwa Aba a jihar Abiya. Daga bisani, sojoji suka mamaye mambobin IPOB inda suka yi amfani da karfi don watsa da tarurrukan sanadiyar wasu suka ji rauni.

Hausawa mazaunar jihar Ribas sun nemi mafaka a ofishin ‘yan sanda bayan wani rikici da IPOB

Hausawa mazaunar jihar Ribas a ofishin 'yan sanda

KU KARANTA: Gwamna Ikpeazu ya sanya dokar hana fita a Aba yayin da sojoji suka dira a garin

Wannan ta haddasa mummunan tashin hankali a tsakanin mambobin IPOB da sojoji wanda kuma hakan ya jagoranci wasu mambobin kungiyar suka sauke fushinsu akan al'ummar Hausawa a yankin, in ji rahotanni.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince

Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince

Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince
NAIJ.com
Mailfire view pixel