Likitoci na so a hana yin tallan taba a Najeriya

Likitoci na so a hana yin tallan taba a Najeriya

- Likitoci sun ce shan taba, giya, da kusalanci ke kashe lafiyar matasa a Najeriya

- Sun ce gwamnati ta fara daukar nauyin masana suna yin bincike a kan cututtuka

- Sun ce gwamnati ta cika alkawarin ta na bawa harkar lafiya kaso 15 daga kudin Najeriya

Saboda yadda taba ke lahanta dan-Adam, likitocin Najeriya, a kasan lemar kungiyar bincike a kan cututtuka (EPISON), suna kira ga gwamnati ta hana ana yin tallan taba a kafofin yada labarai da jikin gine-gine da kuma daukar nauyin wasannin da kamfanonin taba ke yi don suna saka tallan su.

Likitoci na so a hana yin tallan taba a Najeriya

Likitoci na so a hana yin tallan taba a Najeriya

A cikin takardun da kungiyar ta wallafa a karshen taron shekara-shekara na 6 da aka yi a Abuja, EPISON ta ce shan taba, shan giya, rashin cin abinci lafiyayye da kuma kusalanci shi ya sa lafiyar mutane ta ragu, musamman ma lafiyar matasa.

A cikin takardun sun yi kira ga gwamnati da ta cika alkawarin ta na cewa zata na bawa maikatar lafiya kaso 15% daga cikin rabe-raben kudin Najeriya don inganta lafiyar al'umma. Wannan alkwari gwamnati ta dauke shi tun 2001 amma har yau bata cika ba.

DUBA WANNAN: "Za'a kaddamar da sababbin jiragen kasa a digar Abuja-Kaduna a Oktoba." — NRC

Sannan kuma duk da haka tana kira ga gwamnti tana daukar nauyin binciken da masana ke yi a kan cututtuka don kara fahimtar cututtukan don samar da magani.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel