Fafutukar kafa Biyafara ba komai bane ila yunkurin gurgunta mulkin shugaba Buhari - CNG

Fafutukar kafa Biyafara ba komai bane ila yunkurin gurgunta mulkin shugaba Buhari - CNG

- Kungiyar CNG tace masu fafutikan kafa kasar Bayafra na da manufa guda daya ne kawai, shine kawo tangarda a mulkin shugaba Buhari da raba kan 'yan Najeriya

- Kungiyar tayi kira da mutanen arewa kada su dauki doka a hannunsu kuma su guji yadda jita-jita

- Kungiyar arewan tace zata aike da wasiku zuwa ga gwamnatin tarayya da wasu kungiyoyin sa ido a fadin duniya domin hakan ya zama hujja a kotun hukunta masu laifi na duniya

Wata kungiyan tarayyan yan arewa a turance 'Coalation of Northern Groups' CNG tayi ikirarin cewa fafutikan kafa kasar Bayafara da yan kungiyar IPOB ke jagoranta ba komai bane ila zagon kasa domin gurgunta gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da kuma raban kan Najeriya.

Kungiyar ta bada wannan fadi hakan ne a ranar Laraba a wata sanarwa da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun kungiyar, Mr. Abdul-Azeez Suleiman, ya kara da cewa tashin hanakali da masu fafutikan kafa Bayafaran suka haifar ya fara ne a shekara 2015 bayan shugaba Buhari ya dare kan mulki.

Fafutikan kafa Biafra duk yunkuri na gurgunta mulkin shugaba Buhari - CNG

Fafutikan kafa Biafra duk yunkuri na gurgunta mulkin shugaba Buhari - CNG

''Farfado da yunkurin raba Najeriya musamman ta hanyar tashin hankali irin na kungiyar IPOB da sauran irin su daga kudu maso gabashin kasan nan duk yana cikin wata kisa da kisisina da ake kulla wa domin a raba kan mutanen Najeriya har ma da arewa. Anyi amfani da irin wannan a zamanin jumhuriya ta farko amma baiyi nasara ba.'' Inji CNG

DUBA WANNAN: Bayafra: Dalilin da yasa Buhari ya aiko soji suyi min kisan gila - Nnamdi Kanu

Kungiyar cigaba da cewa fafutikan neman kafa kasar Bayafaran zai kara karfafa a shekarar 2018 idan yan siyansu su sa baki a maganan da manufar hanna yin zabe a shekara ta 2109.

Zasuyi kokarin raba kawunan mutane ta hanyar addini da kuma kabilnci. Niyyar su shine arewa ta tanka musu domin rikici ya barke saboda haka ya zama dole yan arewa suyi watsi dasu kadda su taya su cinma manufarsu, dama an san mutanen arewa da hakuri, dattaku da sanin ya kamata.

Kungiyar tace tayi imanin cewa jami'an tsaro zasu iya kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya duk inda suke a kasar nan.

Daga karshe kungiyar yan arewan tace zata aike wasiku zuwa ga gwamnatin tarayya, majalisan dinkin duniya da sauran masu aikin sa ido daga kasashe daban-daban a duniya domin wannan ya zama hujja a kotun hukunta masu laifi na kasa da kasa ICC wanda zai nuna cewa yan kudun ne suke kokarin tada fitina wadda ka iya haifar da kisan kare dangi.

Kungiyar tace zatayi gangami na wayar da mutanen arewa a duk jihohi 19 domin su fahimci sharrin da sauran bangarorin Najeriya ke nufin su dashi kuma suyi watsi da karairayi da jita-jita.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince

Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince

Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince
NAIJ.com
Mailfire view pixel