Lai Muhammed ya zama shugaba a majalisar dinkin duniya reshen yawon shakatawa

Lai Muhammed ya zama shugaba a majalisar dinkin duniya reshen yawon shakatawa

Majalisar dinkin duniya reshen yawan shakatawa (United Nations World Tourism Organisation, UNWTO) ta zabi ministan Labarai da al'adu na Najeriya Lai Mohammed a matsayin mataimakin shugaban majalisar.

An gudanar da wannan zaben ne a ranar Laraba ta yau, bayan zaman tattaunawa na 22 da majalisar ta gudanar a babban birnin Chengdu na gundumar Sichuan dake yankin Kudu maso yammaci kasar Sin.

Kamfanin dillancin labarai NAN (News Agency of Nigeria) ya ruwaito cewa, Ministan wanda ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa kasar Sin, ya zamto shugaban mai wakiltar Najeriya har zuwa shekaru biyu ma su gabatowa.

Lai Muhammed ya zama shugaba a majalisar dinkin duniya reshen yawon shakatawa

Lai Muhammed ya zama shugaba a majalisar dinkin duniya reshen yawon shakatawa

NAN ta ruwaito cewa, kasar Cape Verde tana daya daga cikin kasashe biyu da aka zaba a wannan taro wanda za su wakilci gudanarwar harkokin yawon shakatawa tare da kasar Najeriya.

KU KARANTA: Jihar Kano ta dauki aniyyar yakar fataucin miyagun kwayoyi

Shafin NAIJ.com ta fahimci cewa, akwai kasashen Romania da Switzerland da aka zaba wanda za su wakilci nahiyyar turai, sai kuma kasar Iraq ta za ta wakilci nahiyyar kasashen larabawa da kuma kasar Srilanka mai wakiltar nahiyyar Kudanci Asia.

A jawabinsa, Lai Mohammed ya farin cikinsa ya kuma bayyana cewa tun shekaru 20 da suka gabata ne rabon kasar Najeriya ta samu mai wakiltar ta akan wannan mukami.

Ministan wannan shi yake nuna irin rawar da wannan gwamnatin ta shugaba Buhari ta taka wajen habaka harkokin yawan shakatawa, domin sanadiyar hakan ne ya karawa kasar Najeriya kima da girma a kasashen duniya.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel