Abin tausayi: Matar daya daga cikin ma'aikatan jami'ar Maiduguri da kungiyar Boko haram ke garkuwa da su ta bayyana halin da ita da 'ya'yan ta ke ciki

Abin tausayi: Matar daya daga cikin ma'aikatan jami'ar Maiduguri da kungiyar Boko haram ke garkuwa da su ta bayyana halin da ita da 'ya'yan ta ke ciki

- Mayakan kungiyar boko haram sun kama tare da yin garkuwa da ma'aikatan jami'ar ta Maiduguri tun a watan yuli

- Misis Margaret ta ce mijin na ta direba ne a jami'ar ta Maiduguri

- Yanzu da baya nan yaran mu kullum sai sunyi kuka suna son su yi magana da babansu

Matar daya daga cikin ma'ikatan jami'ar maiduguri da mayakan boko haram ke tsare da su tun ranar 26 ga watan yuli, Misis Margaret Haruna, ta koka kan yadda cigaba da tsaren mijin ta ya jefa ta da 'ya'yanta cikin wahala da kuncin rayuwa. Misis Margaret ta ce mijin na ta direba ne a jami'ar ta Maiduguri kuma ko ranar da za sace shi saida ya kira ta a waya ya rera mata waka domin taya ta murnar zagayowar ranar haihuwar ta.

Abin tausayi: Matar daya daga cikin ma'aikatan jami'ar Maiduguri da kungiyar Boko haram ke garkuwa da su ta bayyana halin da ita da 'ya'yan ta ke ciki

ma'aikatan jami'ar Maiduguri da kungiyar Boko haram ke tsare da su

A bayanin ta, Misis Margaret ta ce "Miji na, Dashe Haruna, mutum ne mai kulawa da iyalin sa sosai domin daga wurin aikin sa sai ya kira mu a waya don jin halin da mu ke ciki. Yanzu da baya nan yaran mu kullum sai sunyi kuka suna son su yi magana da babansu. Ina rokon kungiyar boko haram da su taimaka su sakar min miji na."

DUBA WANNAN: Boko Haram: Ko Kun San Me Gwamnati Ke Yi Da Tubabbun Mayakan Kungiyar Boko Haram?

Mayakan na kungiyar ta boko haram sun kama tare da yin garkuwa da ma'aikatan jami'ar ta Maiduguri tun a watan yuli kuma a halin yanzu dai ba a san halin da su ke ciki ba tun bayan nuna faifan bidiyon su da kungiyar ta yi kwanaki kadan bayan kama su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel