Yanzu Yanzu: Jami’an tsaro sun mamaye jihar Rivers bayan karo da akayi tsakanin sojoji da yan kungiyar IPOB

Yanzu Yanzu: Jami’an tsaro sun mamaye jihar Rivers bayan karo da akayi tsakanin sojoji da yan kungiyar IPOB

- Jami’an tsaro sun amshe wani gari a jihar Rivers

- Wannan ya biyo bayan hari da yan IPOB suka kai ga Hausawa a jihar

- Jami’an tsaron na gudanar da bincike a garin

Jami’in tsaro sun amshe wasu sashin karamar hukumar Oyigbo, musamman a Timber Junction inda aka yi zanga zanga tsakanin sojoji da wasu daga cikin yan kungiyan masu fafatukar neman kafa Biyafara a ranar Talata.

Jami’in tsaron, wadanda suka hada da yan sanda, har da umurnin bincikan motoci domin kiyaye al’amarin da ya auku a baya.

A halin yanzu an samu kwanciyar hankali bayan zanga zangan da ya dauki tsawon awa daya a ranar Talata.

KU KARANTA KUMA: Tambuwal ya nada Dasuki shugaban SIC

A halin da ake ciki, gwamnan jihar Abia, Dr. Okezie Ikpeazu ya sanar da sanya dokar hana fita a Aba, birnin kasuwancin dake jihar kan rashin jituwa dake tsakanin rundunar soji da jama’a.

Operation Python Dance II da rundunar soji ta kaddamar a jihar ya daga hankulan yan kungiyan Biyafara (IPOB) inda suka ki amincewa da aikin sojojin.

Gwamnan jihar yayi jawabi a ranar Talata, 12 ga watan Satumba, inda yace jihar tana sane da daukakar gwamnatin tarayyar Najeriya amman ta nemi rundunar soji ta gabatar da aikin akan doka.

Ya kuma bayyana cewa dokar hana fita zata fara daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a ranar Talata, za’a soke dokar a ranar Alhamis.

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel