Asha! Kashi 50% na malaman makarantun firamare sun fadi jarabawar 'yan aji 4 a Kaduna

Asha! Kashi 50% na malaman makarantun firamare sun fadi jarabawar 'yan aji 4 a Kaduna

- Gwamna Nasir El- Rufai ya bayyana cewa kashi 50% na malaman jihar Kaduna sun fadi jarabawar yan firamare 4

- Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayinda masu sarautun gargajiyan Kudancin Kaduna suka kai masa ziyara

- Gwamnan ya nuna takaicin sa bisa yadda dalibai mata 30 da jihar ta tura kasan waje domin karatun likitanci suka kasa

Gwamna Nasir El-Rufai yace kashi 50% na malaman makarantu a jihar Kaduna sun fadi jarabawar firamare 4 da aka basu a wata gwaji domin tantance wadanda jihar zata sake dauka aiki a matsayi malamai.

El-Rufai ya kara da cewa mafi yawancin daliban da jihar ta aike dasu kasashen waje domin karo ilimi sun dawo a dalilin rashin tabuka abin arziki a makarantun.

Asha! Kashi 50% na malaman makarantun firamare sun fadi jarabawar 'yan aji 4 a Kaduna

Asha! Kashi 50% na malaman makarantun firamare sun fadi jarabawar 'yan aji 4 a Kaduna

Gwamnan ya nuna takaicin sa bisa koro daliban domin a cewarsa kwazon da suka nuna a karatun su na makarantan sakandiri ya nuna alamun zasu iya yin karatun a kasashen waje.

DUBA WANNAN: Rikicin Biafra: 'Yan kungiyan IPOB sun kai hari unguwar hausawa a jihar Ribas

A farkon shekarar bara ne dai Gwamna El-Rufai ya biya wa dalibai mata guda 30 guraben karatu a jami'ar kasar Uganda domin suyi karatun likitanci.

Gwamnan ya bayyana wannan ne a yayinda masu sarautan gargajiya daga kudancin jihar suka kai masa ziyara a gidan gwamnati.

Mai martaba sarkin Jama'a, Alh. Muhammadu Isah Muhammadu ne ya jagoranci tawagar masu sarautun. Sarkin ya nuna farin cikin sa akan bude jami'ar jihar Kaduna da ke kudancin jihar wadda ake rufe a dalilin tashe-tashen hankali a yankin.

Makarantun da aka bude sun hada da kwallejin ilimi na Gidan Waya, Jami'ar jihar Kaduna da kuma Makarantar horar da unguwan zoma da ke Kafanchan.

Masu sarautun sunyi alkawarin cigaba da baiwa gwamatin goyon baya domin ciyar da jihar gaba.

Har ila yau, sun mika wa gwamnan godiya bisa kudi har naira milyan 312 ta gwamnatin sa ta ware domin horar da malaman makarantu a shekarar 2016.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel