Tambayoyi da amsoshi: Tattaunawar Osinbajo da 'yan jarida akan Neja Delta

Tambayoyi da amsoshi: Tattaunawar Osinbajo da 'yan jarida akan Neja Delta

NAIJ.com ta kawo muku yadda tattaunawar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da 'yan jarida ta kasance akan zagayen ziyara da ya ke gudanarwa a yankunan Neja Delta, wanda babban hadimin fadar shugaban kasa akan yada labarai Laolu Akande ya ruwaito a shafin dandalin sada zumunta.

Mataimakin shugaban kasa ya kai ziyara karamar hukumar Ilaje ta jihar Ondo, inda 'yan jarida suka tambayeshi akan manufar wannan ziyara da ya kawowa yankin.

Farfesan ya ka da baki, inda ya bayar da amsar cewa kamar yadda suka sani ya saba gudanar da ziyarce-ziyarce, kuma wannan shine yanki na karshe da ya kawowa ziyara a cikin yankuna masu hako man fetur cikin watannin da suka gabata.

Ya ce, yankin Igbokoda na karamar hukumar Ilaje yana daya daga cikin yankuna masu hako man fetur, kuma wannan ziyara ta zo ne duba da bukatuwar yankin domin ganawa da su.

Tambayoyi da amsoshi: Tattaunawar Osinbajo da 'yan jarida akan Neja Delta

Tambayoyi da amsoshi: Tattaunawar Osinbajo da 'yan jarida akan Neja Delta

Manema labarai sun kara tambayar Osinbajo akan zuwa yaushe ne za gabatar ko kaddamar da bukatun al'ummomin wannan yankuna da yake ziyarta.

Osinbajo ya mayar da amsar cewa, gwamnati ta riga da ta fara kaddamar da wannan aikace-aikace da yankunan suka bukata, kuma tana nan za ta cigaba da gudanarwa kamar yadda ta dauki alkawari.

KU KARANTA: Nnamdi Kanu ya yi sanadin tashi-tashina a jihar Abia - Kungiyar Kudu Maso Gabas

Ya bayar da misalin jami'a mai horar da sanin makamin aiki da ya danganci ruwa wato Maritime University da yankin suka bukata, inda ya ce a watan Oktoba mai kamawa za a bude wannan jami'a.

Akwai matatun man fetur da gwamnatin ta sha alwashin kafawa, wanda a yanzu haka an bayar da lasisin kafa wannan matatu kuma yarjejeniyar gwamnatocin jihar kawai suke bukata a fara gudanarwarsu.

Ya kara da cewa, akwai samar da wutar lantarki da karamar hukumar Ilaje ta bukata, wanda a yanzu gwamnatin ta ware naira miliyan 600 domin kaddamar da wannan aiki. Ya kuma ce, tun shekaru goma da suka gabata aka yi watsi da wannan aiki, amma yanzu ya bayar da tabbacin kammala wannan aiki karkashin wannan gwamnatin ta su.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya yi baƙin cikin rashin Surukin wani tsohon shugaban kasa na Najeriya

Shugaba Buhari ya yi baƙin cikin rashin Surukin wani tsohon shugaban kasa na Najeriya

Shugaba Buhari ya yi baƙin cikin rashin Surukin wani tsohon shugaban kasa na Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel