Boko Haram: Ko Kun San Me Gwamnati Ke Yi Da Tubabbun Mayakan Kungiyar Boko Haram?

Boko Haram: Ko Kun San Me Gwamnati Ke Yi Da Tubabbun Mayakan Kungiyar Boko Haram?

- An sha kira ga gwamnatin Nijeriya da ta yi tayi mai tsoka ga duk mayakin da ya tuba

- Wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun fara saka shakku a kan shirin gwamnati a kan tubabbun mayakan

- Akwai bukatar inganta shirin tsugunar da tubabbun mayakan domin kyautata masu zai dada kwadaitar da masu niyyar tuba

An sha kira ga gwamnatin Nigeria, Musamman lokacin da hare-haren kungiyar boko haram yayi tsamari, da ta yi tayi mai tsoka ga duk mayakin kungiyar da ya tuba, ya ajiye makaman sa. Gwamnatin ta Najeriya ta saurari wannan kira tare da yin amfani da wannan shawarar a wani mataki na mayakan su mika wuya domin a sauya ma su tunani domin dai duk a shawo kan matsalar hare-hare da kungiyar boko haram din ke kaiwa a kasuwanni da makarantu da tasha da sauran wuraren haduwar jama'a.

Boko Haram: Ko Kun San Me Gwamnati Ke Yi Da Tubabbun Mayakan Kungiyar Boko Haram?

Abubakar Shekau

Bayan yin wannnan tayi ga mayakan na boko haram, wani tsagin mayakan sun mika wuya kuma tuni su na tsare a hannun hukumomin gwamnati da abin ya shafa Sai dai wata sabuwa ta bullo, domin a yanzu haka wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun fara saka shakku a kan shirin gwamnati a kan tubabbun mayakan kungiyar ta boko haram. Kungiyoyin sun soki gwamnati da tsare tubabbun mayakan a wurare marasa kyau ba kuma tare da wani tanadi na canja tunanin su da sanin yaushe za a sake su ba. A saboda haka kungiyoyin ke cewa sun lura da akwai bukatar ingantantar shirin tsugunar da tubabbun yan boko haram din domin kyautata masu zai dada kwadaitar da masu niyyar tuban.

DUBA WANNAN: Hukumar soji ta musanta rahoton yin karon batta tsakanin ta da 'yan jarida a Umuahia ta jihar Abia

Wani rahoto da cibiyar dake yaki da ayyukan ta'addanci ta fitar ya nuna cewar kungiyar boko haram ta hure kunnuwan tare da tura yara 'yan kunar bakin wake 434 a tsakanin watan afrilun shekarar 2011 da watan Yunin wannan shekara. Kaso 56 cikin 100, mata ne, sannan kaso 19 cikin 100 ne kanana da matasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel