Kada ku tunzura ta hanyar kai hare-haren fansa – Matasan Arewa sun yi gargadi

Kada ku tunzura ta hanyar kai hare-haren fansa – Matasan Arewa sun yi gargadi

-Wata kungiya daga yankin Arewa ta shwawarci yan Arewa da suyi watsi da hari da aka kai wa al’umman Hausawa dake jihar Rivers

- Kungiyan ta lissafo dalilai da ya kai ga fafatukar neman yankin Biyafara

- Sunyi ikirarin cewa masu fafatukar neman yankin Biyafara suna son kasar ta fada cikin rashin lafiya da rashin tsari

Wata kungiyar matasan Arewa ta bukaci yan Arewa da kada su dauki fansa kan hari da aka kai wa al’umman Hausawa dake jihar Rivers a ranar Talata, 12 ga watan Satumba.

Kungiyan ta bukaci yan Arewa su kwantar da hankulansu kada su kula da irin takalar fadan da tsagerun Biyafara ke yi wa ‘yan Arewa.

Kakakin kungiyar Abdul’Aziz Suleiman ya ce “duk wannan tashe-tashen hankulan da suke yi fa sun tsara shi ne don kasar nan ta dagule nan da 2019, da nufin a samu dalilin faduwar gwamnatin Buhari, ta yadda zaben ma ba zai yiwu ba.”

Kada ku tunzura ta hanyar kai hare-haren fansa – Matasan Arewa sun yi gargadi

Kada ku tunzura ta hanyar kai hare-haren fansa – Matasan Arewa sun yi gargadi

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Aisha Alhassan ta iso Aso Rock don zaman majalisa

Ya na mai cewa, “ya na da kyau mu a nan Arewa mu nuna kawaici kada mu kula su ko yin wata ramuwar gayya, wanda idan aka yi ramuwar gayya, to bukatar su ta hargitsa kasar nan ta biya kenan.

“Irin yadda su ke zakalkalewa su na cewa sai sun kai wa Buhari hari ai wata hila ce da nufin jawo sabon rikici tsakanin yankin Arewa da Kudu-maso-gabas.” Inji Abdul’Aziz.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel