A hukunta sojojin da suka far ma 'yan jarida - Kungiyar CPJ

A hukunta sojojin da suka far ma 'yan jarida - Kungiyar CPJ

- Sojoji sun ragargaza wayoyin hannu da na'urorin 'yan jaridan a garin Umaahia, Jihar Abia

- Rundunar sojoji ta tabbatar da faruwan wannan al'amarin

- Rundunar sojin ta ce lallai sojojin da suka kai farmakin zasu fuskanci ladabtarwa

Kungiyar kare hakkin 'yan jarida, CPJ, ta bukaci a hukunta sojojin da suka far ma 'yan jarida a babban ofishin kungiyar 'yan jarida, NUJ, Jihar Abia. Ta bukaci hakan ne yayin mayar da martani kan jawabin rundunar soja na cewan za su ladabtar da sojojin da suka far ma 'yan jaridan na jihar Abia.

CPJ kungiya ce mai zaman kanta kuma ba ta kasuwanci ba wanda a tsawon shekaru 35 take kare hakkin 'yan jarida ta yadda zasu gudanar sa aikin su ba tare da jin tsoro ba.

A hukunta sojojin da suka far ma 'yan jarida - Kungiyar CPJ

A hukunta sojojin da suka far ma 'yan jarida - Kungiyar CPJ

A ranar talata ne 12 ga watan Satumba, wasu sojojin da aka girke a Umaahia, Jihar Abia, suka far ma 'yan jarida a kan cewa suna daukan su ta bidiyo. An samu rahoton cewa akalla 'yan jarida biyu ne aka far ma a babban ofishin NUJ. 'Yan jaridan sun ce sojojin sun ragargaza wayoyin hannun su da wasu na'urorin su. Wannan al'amari ya faru ne lokacin da sojoji ke kokarin mamaye gidan Nmamdi Kanu.

DUBA WANNAN: Bayafra: Dalilin da yasa Buhari ya aiko soji suyi min kisan gila - Nnamdi Kanu

Mista Oyegoke Badomasi, mai magana da yawun sojoji a Jihar ya ce dan binciken da suka gudanar ya nuna cewan lallai sojojin sun far ma 'yan jarida alhali suna bisa aikin su. Ya kara da cewa tuni dai aka warware matsalar cikin lumana kuma tabbas sojojin da suka kai farmakin zasu fuskanci ladabtarwa.

Shi dai salon aikin soja mai taken ''Rawar Kumurci'' karo na farko ya fara ne a 27 Nuwamba, 2016 ya kuma kare a 27 Desemba, 2016. A kwanan nan ne NAIJ.com ta fitar da abubuwa guda 14 da mutanen yankin Kudu maso Gabas ya kamata su kula da su don kare kai a yayin da rundunar sojoji ke gudanar da wannan salon aikin nasu a yankin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel