Ahir din ku! Masu yada maganganun kiyayya na iya fuskantar shekaru 10 a gidan yari, Ini sifeto janar Idris

Ahir din ku! Masu yada maganganun kiyayya na iya fuskantar shekaru 10 a gidan yari, Ini sifeto janar Idris

- Duk wanda aka kama da kaifin hakan zai iya fuskantar shekaru 10 a kurkuku ko akalla taran naira miliyan 25 ko duk hukunci guda biyun

- Sojoji basu da hurumin yin hukunci kan laifukan da ake gudanar wa a yanar gizo

- Hukumar yada labarai na kasa zata dauki tsattsauran mataki kan kafafen yada labarai masu yada kalamai na kiyayya

Sifeta Janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris ya yi gardin cewa masu yada furucin kiyayya na iya fuskantar gidan yari na shekaru 10 da kuma tara na naira miliyan 25.

Ya yi wannan gargadi ne jiya talata yayin wata tattaunawa da hukumar wayar da kai na kasa, NOA, ta shirya a Abuja. Tattaunawar an shirya ta ne ga masu yada labarai ta yanan gizo kan hatsarin yada maganganun kiyayya.

Ahir din ku! Masu yada maganganun kiyayya na iya fuskantar shekaru 10 a gidan yari, Ini sifeto janar Idris

Ahir din ku! Masu yada maganganun kiyayya na iya fuskantar shekaru 10 a gidan yari, Ini sifeto janar Idris

Jaridar Sun ta bada rahoton cewa shugaban 'yan sandan ya ce Rundunar Soja bata da hurumin hukunci kan laifukan da ake gudanar wa a yanar gizo. Wakilin shugaban 'yan sandan, Mista London Joseph, ne ya fadi hakan. Ya kuma umurci al'ummar Najeriya da su kikaye.

DUBA WANNAN: An bude masana'antar abincin dabbobi da kyankyashe kaji mafi girma a Afrika a Jihar Kaduna

Ya kuma tunatar da masu amfani da kafafen yada labarai na yanar gizo cewan duk wanda aka kama da laifin hakan na iya fuskantar shekaru 10 a kurkuku ko akalla taran naira miliyan 25 ko kuma duk hukunci guda biyun.

Ma'aikatar labarai na kasa, NAN, ta ruwaito cewa hukumar yada labarai na kasa, NBC, a shirye shiryen ta na fuskantar zabe mai zuwa cewa ta yi zata dauki tsattsauran mataki kan duk kafan yada labarai da ke yada maganganun kiyayya.

Shugaban ma'aikatar, Mista Is'haq Kawu ne ya fada hakan ta bakin wakilin sa Mista Armstrong Idachaba a yayin kaddamar da wata tashan rediyo a Jihar Enugu a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel