Wani mai wankin mota ya yi sama da fadi da wata mota a Gwarinpa

Wani mai wankin mota ya yi sama da fadi da wata mota a Gwarinpa

NAIJ.com ta ruwaito cewa, wani mai wankin mota a Gwarinpa ya yi sama da fadi da wata mota kirar Honda Civic da aka kawo masa wankin ta.

Wannan barawo mai suna John ya arce da motar ne bayan da mai ita ya kawo a wanke masa a unguwar First Avenue dake gundumar Gwarinpa a birnin tarayya.

Rahotannin jami'an 'yan sanda sun bayyana cewa, mai motar wanda ya bayar da sunansa na Usman kadai, ya shigar da karar John bayan ya kai ma sa wankin motar ta sa kuma bayan ya dawo karba mota ta ce dauke ni inda ka ajiye ni, domin kuwa babu ita babu alamar John.

Wani mai wankin mota ya yi sama da fadi da wata mota a Gwarinpa

Wani mai wankin mota ya yi sama da fadi da wata mota a Gwarinpa

Daga dai rahotan na 'yan sanda, mai wannan wuri na wankin mota ya yi lakawarin biyan Usman motarsa kafin jami'an 'yan sandan su yi ram da John a makon da ya gabata.

KU KARANTA: Sunayen mutane 20 da suka fi kowa kyauta da sadakar dukiyarsu a duniya

An cafko John tare da wannan mota a garin Kagarko dake jihar Kaduna yayi da yake sharholiyyarsa da ita.

Wani jami'an dan sanda na ofishinsu dake Gwarinpa CSP Nuruddeen Sabo, ya bayar da tabbacin faruwar wannan abu, kuma ya ce binciken jami'an ne ya yi sanadiyar kamo John a garin na Kagarko tare da wannan mota da ya arce da ita.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel