Tsohuwa ýar shekara 70 ta ci duka kan zargin ta da maita, ta maryaga

Tsohuwa ýar shekara 70 ta ci duka kan zargin ta da maita, ta maryaga

Yansandan jihar Bauchi sun cika hannu da wasu mutane 4 da suka lallasa wata mata har ta mutu sakamakon zargin ta da maita a wani kauyen Bauchi, Doka.

Kaakakin rundunar, ASP Kamal Mohammed ya bayyana haka a ranar Talata 12 ga watan Satumba, inda yace wanann lamarin ya auku ne a satin data gabata, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA: Ka daina nuna kwaɗayinka a fili, ba haka ake zama shugaban ƙasa ba – Gwamna Kashim ga Atiku

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Kaakakin yana fadin matasan sun kama matar ne mai suna Liyatu Michael da wata kawarta mai suna Keziya, inda suka kulle su a cikin wani daki, suka dinga jibgarsu

Tsohuwa ýar shekara 70 ta ci duka kan zargin ta da maita, ta maryaga

Wasu matasa

Daga bisani ne Yansanda suka samu rahoton lamarin, indu suka garzaya suka kama matasan su hudu, yayin da sauran kuma suka cika wandonsu da iska, sa’annan suka tafi da gawar matar.

Majiyar tace matsalar ta taso ne a lokacin da matan su biyu suka tabbatar da cewa su mayu ne, kuma sun eke janyo bala’o’i daban daban a kauyen nasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel