Shugaba Buhari ya bayyana matakin daya shirya dauka da ace amfanin gona basu yi kyau ba, Karanta

Shugaba Buhari ya bayyana matakin daya shirya dauka da ace amfanin gona basu yi kyau ba, Karanta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har ya kammala zabar kasar da zai koma gudun hijira da ace amfanin gona basu yi kyau a bara da bana ba, inji rahoton jaridar Leadership.

Buhari ya danganta tunanin barin kasar ne da halin matsin tattalin arziki daya tarar da kasar nan a ciki lokacin daya karbi ragamar mulkin kasar nan, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Shugaban kasa yayi wannan jawabi be a ranar daya karbi bakoncin sarakunan gargajiyan Najeriya a fadar shugaban kasa dake Abuja,inda ya koka kan yadda wasu gwamnoni suka kashe kudaden bashin Paris daya biya jihohi, musamman yadda wasu suka gagara biyan albashi da fansho.

KU KARANTA: Ka daina nuna kwaɗayinka a fili, ba haka ake zama shugaban ƙasa ba – Gwamna Kashim ga Atiku

Shugaba Buhari ya bayyana matakin daya shirya dauka da ace amfanin gona basu yi kyau ba, Karanta

Buhari da sarakunan

Tawagar Sarakunan sun kawo ziyarar ne a karkashin jagorancin mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ada Abubakar da Sarkin Ife, Oba Enitan Ogunwusi.

“Mun ci sa’a a bara da bana an samu ruwan sama mai albarka, da ba dan haka ba kuwa, har na fara tunanin kasar da zan ruga. Amma cikin ikon Allah sai albarkun gona suka yi kyau, dole mu gode ma Allah don da an samu matsaloli da dama a kasar.” Inji Buhari.

Shugaba Buhari ya koka kan rashin biyan albashin ma’aikata a wasu jihohin kasar nan, “Ina sane da matsalolin Najeriya, akwai yan Najeriya da basu samu albashi ba tsawon watanni shida, don haka nake rokon yan Najeriya dasu biya su.”

A nasa jawabin, Sarkin Musulmi yace sun kawo ma Buhari ziyarar ne don nuna godiyarsu ga Allah daya bashi lafiya bayan jinyar da yayi mai tsawo, sa’annan kuma don su shawarce shi daya dage wajen tunkarar kalubalen mulki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Farashin man fetir ya sauko:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel