Nnamdi Kanu ya yi sanadin tashi-tashina a jihar Abia - Kungiyar Kudu Maso Gabas

Nnamdi Kanu ya yi sanadin tashi-tashina a jihar Abia - Kungiyar Kudu Maso Gabas

Sakamakon tashin-tashina da ya afku tsakanin 'yan asalin yankin Biyafara da dakarun soji a jihar Abia, kungiyar yankin Kudu maso Gabashin kasar nan (South East Renewal Group, SERG) ta dora laifin wannan zubar da jini akan shugaban 'yan asalin yankin Biyafara Nnamdi Kanu

A ranar Talatar da ta gabata, an samu rugutsimi tsakanin mabiya Nnamdi Kanu da dakarun soji a babban birni na Umuahia, daura da gida shugaban na IPOB wanda ya sanadiyar rayuka da raunata da dama.

A jawabin kungiyar SERG na safiyar ranar Larabar, shugaban kungiyar Charles Mbani ya na kira ga dukkan shugabannin kabilar Ibo wajen gujewa zartar da yaki a yankin, sa'annan yayi tir da matasan IPOB da cewar, an gurbata musu tunanin su da har ya janyo suke daukan sojin kasa a matsayin abokan adawa.

Kungiyar ta bayyana cewa, wadanda suke daukar nauyin wannan tarzoma da tashin-tashina a yankunan Kudu maso Gabas, ba wasu ba ne face mutanen da suka yi asarar kudadensu wajen cacar cewa sai tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya koma kujerarsa a zaben 2015 da ya gabata.

Nnamdi Kanu ya yi sanadin tashi-tashina a jihar Abia

Nnamdi Kanu ya yi sanadin tashi-tashina a jihar Abia

Sai dai abin takaicin shine, Jonathan ya ci gaba da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa amma wadannan kuwa masu tayar da jijiyoyin wuya sun kasance cikin duhun kai da rashin sanin ciwon kawunansu.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mutane 3 sun hallaka, 20 sun jikkata yayinda rundunar sojin Najeriya sunyi ruwan wuta a gidan Nnamdi Kanu (hoto)

Shugaban kungiyar ya kara da cewa, 'yan siyasar kabilar Ibo da suke marawa Nnamdi Kanu baya su ne suke janyowa wannan matasan suna sadaukar da rayukansu akan abin ba zai amfane su da komai ba sai asara.

Su kuwa jami'an tsaro na yankin Biyafar (Biafra National Guard, BNG) sun ce a shirye suke wajen gwabza yakin da sojin kasa na Najeriya, wanda Charles Mbani ya ke kira da kuma bayar da shawara akan su guji warware wannan shirin na su.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince

Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince

Shugabannin addini ke tunzura yan siyasa yin satar kudin jama’a – Ambode yayi aman wuta, Ezekwesili ta amince
NAIJ.com
Mailfire view pixel