Yanzu Yanzu: Aisha Alhassan ta iso Aso Rock don zaman majalisa

Yanzu Yanzu: Aisha Alhassan ta iso Aso Rock don zaman majalisa

- Ministar dake kula da harkokin mata, Aisha Alhassan a halin yanzu ta halarci zaman majalisa tare da Buhari

- A makon da ya gabata ne Alhassan tace zata goyi bayan tsohon mataimakin kasa Atiku Abubakar ko da Buhari ya bayyana ra’ayin takara a 2019

- Ta kuma bayyana cewa bata shakkan barin majalisar saboda goyon baya da ta nuna wa Atiku

Ministar dake kula da harkokin mata, Aisha Alhassan ta halarci zaman majalisa a yau.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ta isa fadar shugaban kasa a misalin karfe 10:45 da safe.

NAIJ.com ta tattaro cewa taron yan majalisan zai samu shugabancin Muhammadu Buhari wanda za’a fara da karfe 11 na safe.

Yanzu Yanzu: Aisha Alhassan ta iso Aso Rock don zaman majalisa

Yanzu Yanzu: Aisha Alhassan ta iso Aso Rock don zaman majalisa

Alhassan, a zantawa da tayi da BBC a makon da ya gabata, ta bayyana fifiko ga tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar bisa Buhari a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a 2019.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Biyafara ta kaddamar da yaki ga sojoji akan Nnamdi Kanu

Ministan ta fada wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa bata tsoron rasa aikinta, tace “Allah ne mai bayarwa kuma Shine mai karbewa. Shikenan, kuma a hausance na fada.kun san komai na da karshenta.”

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel