Ya zama dole APC ta sasanta tsakanin Atiku da Buhari – Orji Kalu

Ya zama dole APC ta sasanta tsakanin Atiku da Buhari – Orji Kalu

- Orji Uzor Kalu ya bukaci APC da ta sasanta tsakanin Atiku da Buhari

- Wannan ya biyo bayan cewa da Atiku yayi a mayar da shi saniyar ware a jam'iyyar

- Ya kuma bukaci Buhari da ya halarci harkokin jamýyar don sanin abubuwan dake gudana

Tsohon gwamnana jihar Abia, Orji Uzor Kalu, yayi kira ga shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, APC, John Oyegun ya nada Kwamiti da zata sasanta yan jam’iyyan.

Kalu yayi kiran ne yayinda yake bayyana ra’ayinsa ga jawabi da aka yi kan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda yace gwamnatin da Buhari ke shugabanta ta yaye shi bayan amfani da tayi da shi don hawa mulki.

Inda yake magana a ranar Talata a London, dan jam’iyyan APC din ya lura cewa jam’iyyar ne zai iya sasanta rashin jituwan da jam’iyyar take addabe da ita.

Ya zama dole APC ta sasanta tsakanin Atiku da Buhari – Orji Kalu

Ya zama dole APC ta sasanta tsakanin Atiku da Buhari – Orji Kalu

Ya bukaci shugaban kasa ya halarci cikakken harkokin jam’iyyar saboda ya fahimci abubawan da suka shafi yan jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Biyafara ta kaddamar da yaki ga sojoji akan Nnamdi Kanu

Ya karfafa cewa Buhari yana da karfin sasanta rashin jituwar jam’iyyar, shahararren dan kasuwan ya dage cewa dole a sasanta yan jam’iyyar saboda kyakyawan nufin cigaban damokardiyan Najeriya

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel