Kungiyar Biyafara ta kaddamar da yaki ga sojoji akan Nnamdi Kanu

Kungiyar Biyafara ta kaddamar da yaki ga sojoji akan Nnamdi Kanu

- Kungiyar Biyafara ta kasa ta gargadi sojin Najeriya da su janye Operation Python Dance II a yankin kudu-maso-gabas

- Kungiyar tayi ikirarin cewa rundunar soji na niyyar hallaka masu fafatukar Biyafara ne

- Sunyi gargadi cewa baza su bata lokaci ba don ganin sun kare kawunansu idan aka cigaba da kashe-kashe

Kungiyar dake fafutukar neman yancin Biyafara ta gargadi rundunar sojin Najeriya da su kawo karshen aikin Operation Python Dance II da ake cigaba a Kudu-maso-gabas ko kuma yan Biyafaran zasu kwashi makamai domin kare kansu.

A jawabi da aka aiko wa jaridar Daily Post, kungiyar tace aikin sojin a kudu maso gabas dabara ne don ganin an kashe masu yakin neman biyafara a yankin.

NAIJ.com ta fahimci cewa kungiyar tace zata yi adawa da kashe-kashe yan kudu maso gabas din da rundunar soja take yi.

Kungiyar Biyafara ta kaddamar da yaki ga sojoji akan Nnamdi Kanu

Kungiyar Biyafara ta kaddamar da yaki ga sojoji akan Nnamdi Kanu

A halin da ake ciki, gwamnan jihar Abia, Dr. Okezie Ikpeazu ya sanar da sanya dokar hana fita a Aba, birnin kasuwancin dake jihar kan rashin jituwa dake tsakanin rundunar soji da jama’a.

KU KARANTA KUMA: Yan kungiyar IPOB sun kai hari unguwar Hausawa a Rivers (hotuna/bidiyo)

Operation Python Dance II da rundunar soji ta kaddamar a jihar ya daga hankulan yan kungiyan Biyafara (IPOB) inda suka ki amincewa da aikin sojojin.

Gwamnan jihar yayi jawabi a ranar Talata, 12 ga watan Satumba, inda yace jihar tana sane da daukakar gwamnatin tarayyar Najeriya amman ta nemi rundunar soji ta gabatar da aikin akan doka.

Ya kuma bayyana cewa dokar hana fita zata fara daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a ranar Talata, za’a soke dokar a ranar Alhamis.

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel