Daraktan wata ma'aikata ya kashe kan sa ta hanyar rataya

Daraktan wata ma'aikata ya kashe kan sa ta hanyar rataya

- Darakta a wata ministry a jihar Legas ya kashe kan sa ta hanyar rataya

- Har yanzu ba a san dalilin da ya sa ya kashe kan sa ba

- An kai gawar shi mutuware domin binciken dalilin

Wani daraktan ma'aikatan cigaban matasa na jahar legas ya rataye kansa a gidan sa dake Abeokuta, a jihar Ogun a kan dalilin da haryanzu ba'a bayyana ba.

Jami'in hulda da jama'a na 'yansanda na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da haka a ranar Talata da ta wuce, ya ce 'daraktan ya kashe kansa ne bayan ganawa da yaronsa wanda yake fama da ciwon zazzabi.'

Daraktan wata ministiri ya kashe kan sa ta hanyar rataya

Daraktan wata ministiri ya kashe kan sa ta hanyar rataya

Jami'in 'yan sandan ya kara da bayyana yadda mahaifiyar yaron ta kawo masu rahoton, kuma yaron ya bayyana musu da cewa mahaifin sa ya kashe kansa ne misalin karfe 4:00 na yamma bayan ya bashi maganin zazzabi ya sha.

Yaron ya shaida wa jami'an 'yan sanda cewa 'dukkanmu muna gida, bayan ya bani magani sai ya tafi dakin sa. Bayan na jishi shiru zuwa wasu lokuta sai na naje dubashi, sai na sameshi a dakin shi ya rataye kansa da babbar riga.'

DUBA WANNAN: Diyar Osinbajo ta bude gidan kwalliya a Abuja (Hotuna)

Matar daraktan ta ce bata san meye dalilin da yasa ya aikata hakan ba. Suna zaune tare da shi lafiya tun ma da suna wahala sai yanzu da suka sami sauki zai aikata hakan. Ta kara da cewa 'bai nuna mana wata damuwa ko rashin lafiya ba, abin da yasa ya kashe kansa kuma ba wanda ya sani.'

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel